Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Hallaka ’Yan Ta’adda a Katsina da Borno

Sojojin Najeriya Sun Yi Nasarar Hallaka ’Yan Ta’adda a Katsina da Borno

  • Rundunar sojan saman Najeriya ta yi nasarar kashe 'yan ta'adda biyo bayan wani farmaki da ta kai
  • Rundunar ta bayyana adadin 'yan ta'addan da ta yi nasarar hallakawa tare da wuraren da ta hallakasu
  • Jami'in hulda da jama'a na sojojin saman Najeriya ya bayyana abubuwan da suka taimaka masu wurin samun nasarar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A ci gaba da samun nasarar kai hare-hare ta sama da kasa da sojojin Najeriya ke yi, rundunar sojin saman Nigeriya ta yi nasarar hallaka 'yan ta'adda sama da 11 a yankunan Katsina da Borno.

Nigerian Chief of Air Staff, Hasan Abubakar
Shugaban sojojin saman Najeriya, Hasan Abubakar Nigerian Air Force HQ/Facebook
Asali: Facebook

Rundunar sojan saman ta bayyana cewa ta kai farmakin ne karkashin rundunar Operation Hadarin Daji da Operation Hadin Kai a ranakun Jumu'a da Asabar.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri bayan hallaka kasurgumin dan ta'adda da 'yan bindiga suka yi fada

Wuraren da aka kai farmakin

Jami'in yada labaran sojojin saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya bayyana cewa rundunar ta kai tagwayen hare-haren ne a kauyen 'Yar Tsamiya a karamar hukumar Danmusa dake jihar Katsina, inda Rundunar ta hallaka 'yan ta'adda sama da 11.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da kuma kauyen Grazah a karamar Hukumar Gwoza dake jihar Borno inda ta hallaka 'yan ta'adda da dama, kamar yadda sanarwar da rundunar ta fitar ya nuna a shafinta na Facebook.

Jami'in ya kuma kara da cewa rundunar ta yi amfani da jiragen sama ne lokacin da suka hangi 'yan ta'addan na kokarin taruwa a wani yanki mai tsaunuka.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ta yi nasarar lalata makaman da 'yan ta'adda ke amfani da su da wuraren da suka mayar maboyarsu a Grazah.

Kara karanta wannan

Abduljabbar: ’Yan sanda sun bankado shirin kungiyoyin addini da siyasa domin rikita Kano

Dalilan da suka kawo nasarar farmakin sojojin

Rundunar soji ta bayyana samun bayanan sirri a kan ayyuka da maboyar 'yan ta'addan daga cikin abubuwan da suka taimaka masu wurin samun nasara.

Saboda haka suka bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da ba su goyon baya wurin samar masu da bayanan sirri kan ayyukan 'yan ta'adda domin dakile ayyukan su.

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kai irin wadannan hare-haren maboyar 'yan ta'adda da sansaninsu domin rage karfinsu na kai hari kan fararen hula da hukumomi da kuma dakile yunkurin su na renon sabbin 'yan ta'addan.

An kama shugaban 'yan bindiga a Bauchi

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka wani kasurgumin shugaban 'yan bindigan da gungun yaransa suka addabi al'umma a karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi, The Nation ta ruwaito.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an hallaka dan ta'addan mai suna Ya'u ne a wani farmakin da sojojin suka kai maboyarsa a wani yanki da ake kira Burra a Ningi ranar Juma'a.

An kuma ruwaito cewa, Ya'u da yaransa sun addabi yankin na Burra da munanan hare-hare ta hanyar amfani da miyagun makamai tare da sace mutane da neman kudin fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel