Bayan Gama Bincike, Tsohon Gwamnan CBN Ya Gamu da Sabuwar Matsala Babba a Mulkin Tinubu

Bayan Gama Bincike, Tsohon Gwamnan CBN Ya Gamu da Sabuwar Matsala Babba a Mulkin Tinubu

  • Yayin da mai bincike ya kammala aikinsa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya sake shiga sabon kalubale da koma baya
  • Mista Godwin Emefiele zai gurfana a gaban kotu yayin da hukumar yaki da marasa gaskiya EFCC ke yunƙurin ƙara masa tsawon zaman yari
  • Ranar Jumu'a, 4 ga watan Afrilu, EFCC ta hannun lauyanta, Rotimi Oyedepo (SAN), ta kara shigar da tuhuma 26 kan Emefiele

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta shigar da sababbin tuhume-tuhume 26 kan tsohon gwamnan babban banki CBN.

Sababbin tuhume-tuhume da EFCC ta shigar kan Godwin Emefiele sun ƙunshi zargin hannu a cin hanci da almundahana a lokacin da ya jagoranci CBN.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen bincike a babban banki CBN, ya ɗauki mataki

Godwin Emefiele.
EFCC za ta ƙara gurfanar da Emefiele a gaban kotu Hoto: @GodwinIEmefiele
Asali: Twitter

Kamar yadda Channels tv ta tattaro, za a sake gurfanar da Emefiele a gaban babbar kotun jihar Legas da ke zama a Ikeja ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Emefiele zai koma kotu?

Za a sake gurfanar da tsohon gwamnan CBN a gaban kotu bisa laifukan da suka hada da karban na goro, albarkar ofis ta hannun wakilai, da cin hanci da rashawa.

Haka kuma ana tuhumar Emefiele da mallakar kadarori ta hanyar zamba, da bayar da cin hanci da rashawa ga abokan huldarsa wanda ya saɓa dokar cin hanci ta 2000.

A ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu ne mai gabatar da kara na hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN) ya shigar da kwafin takardar sababbun tuhume-tuhumen a kotu.

A rahoton Premium Times, tuhumar farko ta ƙunshi:

Kara karanta wannan

Bobrisky: Kotu ta dauki mataki kan fitaccen ɗan daudu a Legas, ya roki alfarma

"...cewa a tsakanin 2022 zuwa 2023 a jihar Legas, kai Godwin Ifeanyi Emefiele ka ba da umarnin fitar da $2,136,391,737.33 ba tare da bin ƙa'ida ba."

Tinubu ya rufe kwamitin binciken CBN

A wani rahoton kuma kun ji cewa kwamitin binciken da aka naɗa ya kammala bincike na musamman kan ayyukan CBN karkashin tsohon gwamna, Godwin Emefiele.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya godewa Mista Jim Obazee da ƴan tawagarsa bisa namijin kokarin da suka yi wajen gudanar da wannan aiki mai rikitarwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel