2024: Abubuwa 10 da Tinubu Ya Fadawa Najeriya a Jawabin Shiga Sabuwar Shekara

2024: Abubuwa 10 da Tinubu Ya Fadawa Najeriya a Jawabin Shiga Sabuwar Shekara

  • Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabin murnar shiga sabuwar shekara a safiyar 1 ga Junairu
  • Mai girma Shugaban kasa ya tabo batutuwa da yawa a jawabinsa, ya yi alkawarin kawo sauki
  • Shugaba Tinubu ya nuna cewa ya san halin da al’umma su ke ciki, ya ce za a ji dadi a 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabin shigowar 2024 a shafin X, a rahoton nan, mun tsakuro muhimman bayanan da ke ciki.

The Nation ta kawo cikakken jawabin Mai girma shugaban kasa a safiyar Litinin.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya yi jawabin zuwan 2024 Hoto: @Dolusegun16
Asali: UGC

1. Dadi da wahalar 2023

Bola Ahmed Tinubu ya yarda cewa an gamu da kalubale iri-iri a bara duk da an yi nasarar yin zabe har aka karbi gwamnati cikin ruwan sanyi.

Kara karanta wannan

'Dan gida ya fasa kwai, ya jefi Gwamnatin Tinubu da biyewa manufofin turawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Kishin kasa

Tun da aka rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce duk abin da ya yi a ofis, yana duba kishin kasa da maslahar al’umma ne.

3. Wahalar rayuwa

Shugaban kasar ya fadawa al’ummar Najeriya yana sane sarai da ana kuka kan yadda kaya su ka tashi a kasuwa bayan matsalar rashin aikin yi.

4. Garkuwa da mutane

Ba tare da ana surutu ba, gwamnatin Bola Tinubu ta kubutar da mutane da yawa kamar yadda shugaban kasar ya fada daga hannun ‘yan bindiga.

5. Tattalin arziki

Jawabin shugaban kasar na shiga shekarar 2024 ya ce an yi shimfidar farfado da tattalin arzikin kasa a 2023, ana jiran a fara cin moriyar tsarinsa.

6. Wutar lantarki

Jaridar ta ce haduwar shugaba Tinubu da Olaf Scholz a taron COP28 ya bada dama an sake karfafa maganar samar da wutar lantarki a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Alkawaran iska": NLC ta mayar da martani mai zafi ga Tinubu, ta fada masa abu 1 da zai yi

7. Fetur da matatun mai

Gwamnati mai-ci ta dage wajen ganin an fara tace mai a gida, matatar Fatakwal ta fara aiki, haka zalika matatar Dangote za ta fara samar da fetur.

8. Abinci

A shekarar nan ta 2024, shugaba Tinubu ya yi alkawari za a noma eka 500, 000 domin a samu masara, shinkafa, alkama, gero da sauran hatsi.

9. Ma'aikata ayyukan yi

Gwamnatin APC za ta bada karfi a 2024 wajen saukaka kasuwanci da kawo ayyukan yi a kasa kuma za a kara albashin ma'aikatan Najeriya.

10. Wadanda aka ba mukamai

A karshe shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba zai bari wadanda aka ba mukamai su gagara tabuka komai ba, za a rika lura da kokarin kowa.

2024: Kiran Atiku ga Tinubu

Rahoton nan ya nuna Atiku Abubakar yana so Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da tsaro a Najeriya da aka shiga shekarar 2024.

‘Dan takaran na PDP a zaben shugaban kasa ya yi tir da yadda aka kashe Bayin Allah a Filato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel