Yunwa Ta Ci ’Yan Bindiga Yayin da Suka Farmaki Rumbun Abinci a Jihar Arewa, an Dauki Mataki

Yunwa Ta Ci ’Yan Bindiga Yayin da Suka Farmaki Rumbun Abinci a Jihar Arewa, an Dauki Mataki

  • Yayin da ake cikin halin kunci a Najeriya, ‘yan bindiga sun yi yunkurin kai hari kan rumbun Gwamnatin Tarayya da ke jihar Katsina
  • Jami’an tsaron NSCDC sun yi nasarar dakile harin kan rumbun da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar Katsina
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Buhari Hamisu ya fitar a jiya Asabar 6 ga watan Afrilu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina – Jami’an hukumar NSCDC sun yi nasarar dakile harin da ‘yan bindiga suka kai kan ma’ajiyar abinci a jihar Katsina.

Jami’an sun yi nasarar dakile harin ne a jiya Asabar 6 ga watan Afrilu a karamar hukumar Dutsinma da ke jihar, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Murna yayin da malamin Musulunci da aka sace a jihar Arewa ya shaki iskar 'yanci

'Yan bindiga sun farmaki rumbun abincin gwamnati a jihar Arewa
Jami'an tsaro sun dakile harin 'yan bindiga kan rumbun abinci a jihar Katsina. Hoto: Umar Dikko Radda.
Asali: Facebook

Yaushe 'yan bindigan suka farmaki rumbun abinci?

Kakakin hukumar, Buhari Hamisu shi ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce jami’ansu sun dakile harin da misalin karfe daya na dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hamisu ya ce ‘yan bindigan sun yi yunkurin lalata ma’ajiyar abincin ne domin sace manajan mai suna Lawal Shittu ‘Yar’adua.

Ya ce jami’ansu sun yi nasarar dakile harin inda suka shafe fiye da awanni biyu suna bata-kashi da ‘yan bindigar.

“Jami’anmu sun yi nasarar fin karfin ‘yan bidigan wadanda suka tsallaka katangar rumbun abincin inda suka tsira da raunuka.”
“Rumbun abincin bai samu matsala ba sannan maharan ba su yi nasarar yin aika-aikar da suka yi niyyar yi ba.”

- Buhari Hamisu

An tsaurara tsaro a rumbunan abincin

Kakakin rundunar ya ce jami’ansu sun kara turo jami’an tsaro wurin domin tabbatar da inganta tsaron rumbun, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

PDP: Kungiyoyi sun ambaci Minista a cikin wadanda za a ladabtar saboda cin amana

Ya ce ana amfani da rumbun ne domin rarraba kayan hatsai ga mutanen jihohin Katsina da Zamfara da kuma Sokoto.

Tsagera sun fasa rumbun abinci a Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa wasu matasa a jihar Kebbi sun farmaki wani rumbun ajiyar abinci a unguwar Bayan Kara da ke Birnin Kebbi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kai farmakin ne a ranar Asabar da ta gabata inda suka daka wawa kan kayan abincin.

Wannan na zuwa ne yayin da jama’ar kasar ke cikin wani irin yanayi na tsadar rayuwa tun bayan tsare-tsaren tattalin arziki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel