'Yan bindiga sun kashe Manajan kamfanin da Buhari ya bude a Kano
A daren Alhamis 28/12/2017 wasu mahara suka kaddamar da kisan gilla ga dan kasuwa Alhaji Sule Itas/Gadau da ake yi wa lakabi da Lauya.
Kafin rasuwar sa shine Manajan kamfanin Gerawa Global Construction Company Limited, babban kamfanin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude yayin ziyarar jihar Kano. Maharan sun kashe shi ne a gidan sa dake unguwar Tokarawa a jihar Kano.
Legit.ng ta samu daga majiyar mu ta Arewa Post cewa an bayyana mamacin a matsayin mutumin kirki da ya ke taimakawa talakawa da marasa karfi. Inda ya fito da tsarin rubuta sunayen magidanta da marasa Galibu da ake aika musu da kayan abinci.
An yi jana'izar sa a garinsu Zakwaran Itas/Gadau da ke jihar Bauchi. Allah Ya Jikan sa Ya kuma gafarta masa Kura-kuransa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng