Gwamnatin Katsina Ta Karbo Sabon Bashi? Dikko Radda Ya Yi Wa Hukumar DMO Martani

Gwamnatin Katsina Ta Karbo Sabon Bashi? Dikko Radda Ya Yi Wa Hukumar DMO Martani

  • Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Radda ya ce rahoton hukumar kula da basussuka (DMO) kan gwamnatin jihar ba gaskiya bane
  • Rahoton ya nuna cewa gwamnatin jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka karbi sabon bashi wanda hakan ya kara ta'azzarar bashi a jihohin
  • Sai dai da yake martani a cikin wata sanarwar, Gwamna Raddan ya ce tun da ya hau mulkin Katsina bai taba ciwo bashin ko kwabo ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Katsina - Gwamnan Katsina, Mallam Dikko Radda ya musanta rahoton hukumar kula da basussuka ta kasa (DMO) na cewa yana cikin gwamnonin da suka karbo sabon bashi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Sokoto ta ciyo bashin makudan kudi? Gwamna Ahmed ya fayyace gaskiya

Gwamnan Katsina ya yi magana kan karbo sabon bashi
Dikko Radda ya ce akwai kuskure a rahoton hukumar kula da basussuka ta kasa. Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

"Har yanzu muna biyan bashi - Radda

Jaridar Leadership ta ruwaito gwamnan a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ibrahim Mohammed ya fitar, ya ce akwai kuskure a rahoton hukumar DMO.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jadda cewa tun da gwamnatin Radda ta fara mulki a Katsina take biyan basussukan da ta gada daga gwamnatocin baya.

Sanarwar ta kuma ce har yanzu yanzu gwamnatin APC mai ci a jihar Katsina karkashin Gwamna Radda ba ta ciwo bashin ko kwabo ba.

Gwamnatin Radda ta karbo sabon bashi?

A cewar sanarwar:

"Kuma ba wai mun ce gwamnatin jihar ba za ta ciwo bashi nan gaba ba, za ta iya yin hakan a duk lokacin da bukata ta taso.
"Amma a halin yanzu, babu wanda ke bin gwamnatin mu bashi. Yayin da muke kokarin kamanta gaskiya da adalci, muna ba da hajuri ga wadanda wannan rahoto ya bata wa rai."

Kara karanta wannan

Jerin sabbin gwamnonin Arewa 7 da suka karbi bashin biliyoyi cikin watanni 6 kacal

Jaridar This Day ta rahoto Gwamna Radda yana kira ga kafofin watsa labarai da su goyi baya tare da tallafa wa gwamnatin jihar a kokarinta na inganta rayuwar 'yan jihar.

Sanarwar ta kuma kara jaddada manufofin gwamnatin APC a jihar Katsina na samar da ayyukan more rayuwa da saukaka wa jama'a.

Radda ya gwangwaje ma'aikatan Katsina

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya ba da umarnin sakarwa ma'aikata N15,000 domin yin hidimar azumi da Sallah.

Gwamnan ya ce a raba kudaden ga ma'aikatan jiha da na kananan hukumomi, domin rage masu radadin matsin tattalin da kasar ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel