Emefiele: Shugaba Tinubu Ya Kawo Karshen Bincike a Babban Banki CBN, Ya Ɗauki Mataki

Emefiele: Shugaba Tinubu Ya Kawo Karshen Bincike a Babban Banki CBN, Ya Ɗauki Mataki

  • Shugaban ƙasa ya bayyana ƙarshen aikin kwamitin da ya gudanar da bincike a babban banki CBN karkashin Godwin Emefiele
  • Bola Tinubu ya godewa Mista Jim Obazee da ƴan tawagarsa bisa namijin kokarin da suka yi wajen gudanar da wannan aiki mai rikitarwa
  • Kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya godewa Mista Jim Obazee, bisa aikin da ya yi a matsayin mai bincike na musamman na babban bankin Najeriya (CBN) da sauran hukumomi masu alaka.

Bayan haka ne Shugaban Ƙasa Tinubu ya bayyana cewa an ƙarƙare binciken a hukumance.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗauki zafi kan rikicinsa da ministan Tinubu, ya faɗi dalilin amincewa da sulhu

Shugaba Bola Tinubu.
Tinubu ya karkare aikin binciken da aka yi a CBN Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024 a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta nakalto Shugaban kasar yana yabawa Mista Obazee saboda kwazon da ya nuna da kwarewa wajen tafiyar da “wannan muhimmin aiki na kasa mai matuƙar rikitarwa.”

Yaushe Obazee ya gama bincike a CBN?

Ngelale ya bayyana cewa kwamitin binciken karƙashin Mista Obazee ya kammala aikinsa ne ranar 31 ga watan Maris, 2024, bisa haka Tinubu ya rufe shi a hukumance.

A cewarsa, tuni hukumomin tabbatar da bin doka da oda suka fara ɗaukar matakan da suka dace a rahoton da Obazee ya haɗa dangane da abubuwan da suka faru a CBN.

“Shugaban kasa ya godewa Mista Obazee bisa amsa kiran aikin da ya yi tare da yi masa fatan samun nasara a dukkan ayyukansa na gaba."

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi abin da zai hana Tinubu yin shekara 8 kan karagar mulki

- Ajuri Ngelale.

Yadda Tinubu ya naɗa kwamitin

Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin soshiyal midiya ya wallafa wannan sanarwa a shafinsa na manhajar X wadda aka fi sani da Twitter.

A watan Yuli, 2023 Tinubu ya nada Obazee, tsohon babban jami’in hukumar bayar da rahoton kudi ta Najeriya (FRC), domin ya binciki ayyukan CBN karkashin tsohon Gwamna, Godwin Emefiele.

Sakamakon tarin abubuwan da Obazee da ƴan tawagarsa suka gano, a yanzu tsohon gwamnan CBN na ci gaba da funkantar shari'a a gaban.kotu.

A rahoton da ya miƙa wa Tinubu, Obazee ya gano almundahanar makudan kuɗade, kamar cire kuɗi da bisa ƙa'ida ba da sauran badaƙaloli masu yawa.

Da gaske Dala ta karye zuwa N650?

A wani rahoton kuma Wani fitaccen mai amfani da X ya yi ikirarin cewa Dala ta ƙara karyewa zuwa N650 yayin da mutane suka fara sayar da Dalar da suka ɓoye.

Wani shafin yanar gizo mai tsage gaskiya ya gudanar da bincike kan sahihancin wannan ikirari kuma ya wallafa rahotonsa ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel