Lamunin Karatu: Tsare Tsaren da Gwamnati Ta Yi Na Fara Ba Dalibai Rancen Kudi
- Gwamnatin tarayya ta ce za ta kaddamar da asusun ba da lamunin karatu ta hanyar yin gwajin shirin ga daliban manyan makarantu
- A ranar Laraba ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kudurin dokar kafa asusun lamunin wanda a yanzu ya zama doka
- Gwamnati ta bayyana cewa nan gaban kadan Tinubu zai nada shugabannin da za su jagoranci tafiyar da lamuran asusun na shekaru biyar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta bayyana tsarinta na fara gwajin sabuwar dokar ba da lamunin ilimi ga dalibai.
Asusun bayar da lamuni ga daliban Najeriya, a ranar Laraba ya ce za a fara kaddamar da shirin ne da daliban manyan makarantun gwamnati na kasar.
Mai magana da yawun asusun, Mr. Nasir Ayitogo, ya tabbatar da hakan a ranar Laraba, inda ya zayyana dokokin da asusun zai yi aiki a kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makarantun da za su amfani da shirin
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Ayitogo ya ce manyan makarantun gwamnati sun hada da jami'o'in tarayya da na jihohi, da kwalejin fasaha da na ilimi.
Ayitogo ya ce:
"A matakin fara gwajin shirin, manyan makarantu na gwamnati ne kawai za su amfana, ban da na kudi."
Tsarin nada shugabannin asusun lamunin
A cikin sabuwar dokar, akwai bukatar kafa hukumar kula da asusun ba da lamunin da za ta rinka karbar kudi daga gwamnati, raba kudi ga daliban manyan makarantu.
Haka zalika, dokar za ta sa samar da shugaban asusun, manaja, daraktoci guda biyu a bangaren kudi da na gudanarwa da za su taimaka shugaban ya tafiyar da harkokin asusun.
Dokar ta ba shugabannin damar yin aiki na tsawon shekaru biyar, inda wa'adin su zai kare.
Kowanne dalibi zai iya karbar rancen kudin
Dokar ta kuma ba hukumar asusun damar kulla yarjejeniyar ba da lamuni ga dalibai, da kuma karfin ikon daukar mataki kan wadanda suka ki mayar da bashin da aka basu.
Sai dai har yanzu ba a sanya ranar da shugaban kasar zai kaddamar da shirin ba, amma dai mai magana da yawun asusun ya ce dalibai za su cike bukatar karbar bashin ne a shafin asusun.
A cewar jaridar The Cable, Tinubu a lokacin da ya rattaba hannu kan kudirin dokar ya ce babu wani dan Najeriya da za a cire shi daga tsarin bayar da lamunin ilimin.
Daliban da ba za su samu lamuni ba
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa ba dukkan dalibai ne za su samu lamunin karatu da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta fara bayarwa ba.
Kamar yadda binciken mu ya nuna, akwai jerin dalibai biyE da ba su cancanci samun tallafin ba, kuma gwamnati ya cire su daga wadanda za ta ba lamunin.
Asali: Legit.ng