Bashin Dalibai: Jerin Mutum 5 da Gwamnatin Tinubu Ba Za Ta Ba Su Rancen Ba

Bashin Dalibai: Jerin Mutum 5 da Gwamnatin Tinubu Ba Za Ta Ba Su Rancen Ba

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, 3 ga Afrilu, ya rattaɓa hannu kan ƙudirin dokar bayar da lamuni ga ɗalibai wanda aka yi wa garambawul
  • Fadar shugaban ƙasan ta ce shirin bada lamuni ga ɗaliban zai taimaka wajen ganin an samu ci gaba a harkar ilmi a ƙasar nan
  • Sai dai, ba dukkan ɗalibai ba ne suka cancanci wannan shiri da aka yiwa laƙabi da wanda ba a taɓa yin irinsa ba a tarihin ilimi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu, ya sanya hannu a kan ƙudirin dokar bayar da bashi ga ɗalibai wanda ya zama doka.

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa gwamnatin Tinubu ta shirya ninka kudin wutar lantarki

Manufar gwamnatin tarayya ita ce bayar da tallafin kudi ga ɗaliban Najeriya marasa galihu a manyan makarantun gaba da sakandare.

Tinubu ya ss hannu kan kudirin dokar ba dalibai bashi
Akwai dalibai da ba za su amfani da shirin bada bashi na Tinubu ba Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

An fahimci cewa tsarin zai bada lamuni ga ɗalibai don biyan kuɗin karatu da sauran kuɗin makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani abin da aka bayyana a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin ilimi a Najeriya, Dada Olusegun, mai taimaka wa shugaban ƙasa ya ce ɗalibi mai kwas na shekara huɗu a karatun digiri na iya samun bashin Naira miliyan biyu.

Waɗanne ɗalibai ne ba za su amfana ba?

Sai dai, akwai mutane biyar da aka ware waɗanda ba su cancanci a ba su wannan bashin ba.

Jaridar Nigerian Tribune ta jero mutanen da ba su cancanci samun rancen ba. Ga jerinsu nan ƙasa:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon farmaki a jami'ar Arewa, sace dalibai

1. Ɗalibin da aka samu da laifin yin satar jarabawa.

2. Ɗalibin da aka samu ya ƙi biyan wani bashi da ya taɓa karɓa a baya.

3. Ɗalibi mai tarihin aikata laifin kisa ko wani laifi da ya shafi rashin gaskiya ko zamba.

4. Ɗalibin da iyayensa (mahaifi ko mahaifiya) suka kasa biyan wani bashi na ɗalibai ko wani rance da aka taɓa ba su a baya.

5. Ɗalibin da aka yankewa hukunci kan laifin da ya shafi harkokin ƙwaya.

ASUU tana adawa da tsarin rancen dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ASUU reshen jihar Bauchi, ta jaddada ƙudirinta na ƙin amincewa da ba ɗalibai bashi.

Ƙungiyar ta ASUU ta yi nuni da cewa maimakon a ba ɗaliban rancen kuɗi, kamata ya yi gwamnati ta ba su tallafin karatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel