Abin da Remi Tinubu Ta Fadawa Matan Tsoffin Shugabannin Najeriya Yayin Buda Baki

Abin da Remi Tinubu Ta Fadawa Matan Tsoffin Shugabannin Najeriya Yayin Buda Baki

  • Matar shugaban kasar Najeriya, Remi Tinubu ta bukaci dukkan jama’ar kasar da su hada kai domin inganta ta
  • Remi ta ce mai gidanta, Bola Tinubu ya na dukkan mai yiwuwa domin ganin ya inganta kasar fiye da yadda ya same ta
  • Uwargidan shugaban ta bayyana haka ne yayin buda baki da matan tsoffin shugabannin kasar da matan gwamnoni a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Uwargidan Shugaba Tinubu, Oluremi Tinubu ta bayana cewa shugaba kasar ya na duk mai yiwuwa domin inganta Najeriya.

Remi ta ce a kullum kokarin Tinubu shi ne yadda zai kawo sauyi a kasar fiye da yadda ta ke a yanzu.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya bayyana hanyar da ƴan adawa za su iya tsige shi daga mulki

Remi Tinubu ta fadi kokarin da shugaban kasa ke yi domin inganta al'umma
Remi Tinubu ta bayyana kokarin da Bola ke yi kan inganta Najeriya. Hoto: Oluremi Tinubu.
Asali: Facebook

Alkawarin da ta dauka kan inganta Najeriya

Ta ce kafin kammala wa’adinsa a matsayin shugaban kasa, Tinubu zai tabbatar da ya inganta kowane bangare a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar shugaban kasa ta bayyana haka ne yayin buda baki da matan tsoffin shugabannin kasa da kuma na gwamnoni a Abuja.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimarta, Busola Kukoyi ta fitar a yau Lahadi 31 ga watan Maris.

“Shugaban kasa zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da gina kasar Najeriya lokacin da zamu bar wannan wuri.”
“Dukkanmu mu na da gudunmawar da za mu bayar domin tabbatar da daura wannan kasa ta mu kan turba mai kyau.”

- Remi Tinubu

Remi ta ce gwamnatin Tinubu ta kawo tsare-tsaren da za su ragewa al’ummar kasar radadin da suke ciki.

Shawarar da matar Kashim ta bayar

Kara karanta wannan

Ana daf da buda baki, Buhari ya tura sako ga Tinubu, ya yi masa ruwan addu'o'i

Tun farko a jawabinta, matar mataimakin shugaban kasa, Nana Kashim Shettima ya bukaci dukkan mata su zama masu son junansu.

Ita ma ta bukaci hadin kai daga dukkan jama’ar kasar domin samun ci gaba musamman a wadanna kwanaki 10 masu albarka.

Remi Tinubu ta ce bata tsoron mutuwa

Kun ji cewa uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu ta ce a yanzu ko kadan ba ta tsoron mutuwa ta dauke ta.

Remi ta bayyana haka ne a jihar Bauchi yayin da ta kai ziyara jihar domin gudanar da wasu ayyuka.

Wannan na zuwa ne bayan wani malamin Musulunci ya yi mata barazanar kisa a matsayinta na wacce ba Musulma ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel