Ku kara farashin mai, ku kara kudin haraji: Asusun lamuni IMF ya jaddada kira ga gwamnatin Najeriya

Ku kara farashin mai, ku kara kudin haraji: Asusun lamuni IMF ya jaddada kira ga gwamnatin Najeriya

  • Karo na uku, asusun lamunin duniya na bada shawaran ayi gaggawan cire tallafin man fetur
  • Ministar kudin Najeriya ta bayyana adadin kudin da kamfanin NNPC ta bukata na kudin tallafin mai
  • Wannan ya biyo bayan dakatad da shirin kara farashin mai da gwamnatin tarayya tayi ranar Litinin

Amurka - Makonni biyu bayan dakatad da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya tayi, asusun lamunin duniya IMF ya sake kira ga Najeriya tayi gaggawa cire tallafin man fetur.

Idan Gwamnati ta cire tallafin mai, farashin litan mai zai yi tashin gwauron zabo.

IMF ya bayyana hakan a shawara da shugabanni kan 'Article IV' tare da hadin kan Najeriya da aka saki ranar Litinin.

Legit ta samu takardan shawarar ne a shafin yanar gizon IMF.

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

A cewar takardan:

"Diraktocin na kira ga cire tallafin mai, tare da bada kudin rage zafi kan talakawa da kuma amfani da raran kudin yadda ya kamata."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sun yi kira ga fadada samar da kudin shiga wanda ya hada da kara kudin harajin VAT, tabbatar da mutane na biyan kudin haraji."

Man fetur
Ku kara farashin mai, ku kara kudin haraji: Asusun lamuni IMF ya jaddada kira ga gwamnatin Najeriya Hoto: NNPC
Asali: UGC

Zamu rikirkita Najeriya idan aka kara farashin fetur da lantarki, NLC

Kungiyar Kwadagon Najeriya NLC, ta lashi takobin cewa yan Najeriya ba zasu yarda da wani sabon karin farashin man fetur ba da sunan cire tallafin mai.

NLC ta yi kira ga ma'aikata da yan Najeriya su shirya zanga-zanga kan wannan abu da gwamnati ke shirin yi.

Majalisar tattalin arzikin Najeriya NEC ta baiwa gwamnatin tarayya shawarar a kara farashin litan man fetur zuwa N302 nan da watan Febrairu 2022.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

Wannan shawara na cikin jeringiyar shawarin da kwamitin NEC mai tattaunawa da kamfanin mai NNPC kan farashin man da ya kamata a sanya a Najeriya ta bada, rahoton TheCable.

Wannan kwamiti dake karkashin jagorancin gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ta gabatar da shawarin.

Kamfanin man feturin Najeriya (NNPC) ta bukaci kudi N3 trillion daga wajen gwamnatin tarayya matsayin kudin tallafin man fetur na 2022 tun da an fasa kara farashin mai.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a fadar Shugaban kasa bayan zaman majalisar zartaswa FEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel