Dakarun Sojoji Sun Sake Yin Ajalin Hatsabibin Ɗan Bindiga da Mayaƙansa a Zamfara

Dakarun Sojoji Sun Sake Yin Ajalin Hatsabibin Ɗan Bindiga da Mayaƙansa a Zamfara

  • Kasurgumin dan ta'adda a jihar Zamfara ya gamu da ajalinsa bayan dakarun sojoji sun hallaka shi da mayaƙansa
  • Rundunar sojojin ta bayyana nasarar da ta samu inda ta murkushe hatsabibin dan ta'addan, Junaidu Fasagora da mayakansa
  • Sojojin sun sanar da wannan nasara a yammacin yau Laraba 27 ga watan Maris a shafin X da aka fi sani da Twitter

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar ganin bayan wani hatsabibin dan ta'adda a jihar Zamfara.

Rundunar ta ce ta yi ajalin kasurgumin dan ta'addan mai suna Junaidu Fasagora da sauran wasu na hannun damansa.

Sojoji sun yi ajalin kasurgumin ɗan bindiga a Zamfara
Kasurgumin ɗan bindiga ya gamu da ajalinsa bayan sojoji sun hallaka shi a Zamfara. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Nasarar da sojoji suka samu a Zamfara

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 17: Tinubu ya fusata, ya ba da sabon umarni ga dattawa da sarakunan Okuama

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa sa rundunar ta fitar a shafinta na X a yammacin yau Laraba 27 fa watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakarun sojojin sun samu nasarar murƙushe Junaidu da sauran mayakansa ne a yankin karamar hukumar Tsare da ke jihar.

Sojojin suka ce Fasagora da mayakansa sun addabi yankin Arewa maso Yamma da ayyukan ta'addanci.

Sojojin sun sha alwashin kakkabe 'yan bindiga

Dakarun suka ce yin ajalin wadannan miyagu babbar nasara ce ganin yadda suka yi sanadin rasa rayukan al'umma da asarar dukiyoyi.

Rundunar ta ce wannan nasara ya tabbatar da himmatuwarsu wurin wanzar da zaman lafiya musamman a yankin Arewa maso Yamma.

Ta sanar da ci gaba da dakile ayyukan ta'addanci a yankunan domin maido da zaman lafiya musamman a wuraren da suke fama da matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Abubuwan sani 5 dangane da jana'izar da za a yi wa jami'an tsaron

Arewa maso Yammacin Najeriya na fama da hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa musamman a yankunan karkara.

Yan bindiga sun hallaka babban limami

Kun ji cewa Wasu 'yan bindiga sun yi ajalin Sheikh Ahmad Rufa'i, babban limamin masallacin Juma'a da ke ƙauyen Keita a ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Lamarin ya faru ne makwanni uku kacal bayan kisan da aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada da ke ƙaramar hukumar Gusau a jihar.

Daga bisani gwamnatin jihar ta sanar da cafke wasu 'yan sa kai da ake zargin da hannunsu a kisan Sheikh Mada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel