An Budewa Tawagar Motocin Gwamnan Delta Wuta, An Kashe Yan Sanda 3, Gwamnan bai cikin Motar

An Budewa Tawagar Motocin Gwamnan Delta Wuta, An Kashe Yan Sanda 3, Gwamnan bai cikin Motar

  • Wasu yan bindiga da ba'a gane su wanene ba sun budewa tawagar motocin gwamnan Delta wuta
  • Gwamna Okowa shine dan takarar kuejrar mataimakin shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP
  • Gwamnan ya yi alhinin mutuwar wadanda yan sandan kuma ya jajintawa iyalansu

Asaba - Jami'an hukumar yan sanda uku sun rasa rayukansu sakamakon harin da wasu yan bindiga suka kaiwa tawagar motocin gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP, Ifeanyi Okowa.

An tattaro cewa wanda abu ya auku ne ranar Juma'a a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra yayinda gwamnan ke hanyarsa ta zuwa jihar Abia.

An bayyana sunan yan sandan matsayin Lucky Aleh, Celestine Nwadiokwu da Jude Obuh.

An kai musu harin ne misalin karfe 1:30 na rana kuma aka bankawa motarsu wuta, rahoton SaharaReporters.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kwato Wani Matashi Karfi Da Yaji Hannun Yan Sanda Kan Batanci ga Al-Qur'ani, Sun Kasheshi

Yan sanda 3
An Budewa Tawagar Motocin Gwamnan Delta Wuta, An Kashe Yan Sanda 3, Gwamnan bai cikin Motar Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wani ma'aikacin gidan gwamnatin jihar,

"Yan sanda hudu ke cikin motar amma daya na sanye da kayan gida saboda haka basu kasheshi ba, suka sakeshi."

Kakakin hukumar yan sandan jihar Anamra, Ikenga Tochukwu, wanda ya tabbatar da lamarin yace:

"Mun samu kira kuma muka garzaya wajen. Yan sandan da aka kashe daga jihar Delta suke kuma sun kan hanya ne."

Jawabin gwamnan Delta

Gwamnan jihar Delta ya aike sakon ta'aziya ga hukumar yan sandan jihar da iyalan yan sandan uku.

A ranar Asabar, gwamnan ya yi hira da manema labarai inda ya bayyana alhininsa bisa abinda ya faru.

Ya ce yan sandan sun bi wata hanya daban sabanin wacce sauran suka bi kuma nan aka bude musu wuta.

Ya bayyana hakan ta bakin kwamishanan yada labaran jihar, Charles Aniagwu, a cewar SR.

Kara karanta wannan

An Kama Wanda Ya Kai Wa Tawagar Matar Gwamnan Adamawa Hari

Ya ce:

"Mun kawo muku labarin takaici na mutuwar jaruman yan sandanmu uku da suka taimaka wajen samar da zaman lafiya a jiharmu. Yan sandan sun gamu da ajalinsu yayinda suke hanyar tafiya wajen kamfen PDP a Abia."
"Wadannan yan sanda sun raba hanya da sauran inda suka bi wata hanyar daban. An bude musu wuta a titin Ihiala-Orlu hanyar Umuahia kuma aka kashesu cikin rigar sarki, yayinda mutum daya dake sanye da kayan gida ya arce."
"Muna gano gawawwakinsu kuma mun tuntubi iyalansu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel