Bayan Kashe Sojoji a Delta, An Sake Hallaka Jami'an 'Yan Sanda a Wani Harin Kwanton Bauna

Bayan Kashe Sojoji a Delta, An Sake Hallaka Jami'an 'Yan Sanda a Wani Harin Kwanton Bauna

 • Wasu mahara ɗauke da makamai sun kashe jami’an ‘yan sandan Najeriya shida a wani harin kwantan ɓauna a jihar Delta
 • Rundunar ƴan sandan ta yi alƙawarin karrama jami’an da suka mutu, a bikin karrama jami'anta da bada lambar yabo a watan Afrilun 2024
 • IGP Egbetokun ya kuma ba da umurnin a gaggauta cafko waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin, tare da biyan haƙƙoƙin jami’an da aka kashe ga iyalansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da rasa jami’anta guda shida a wani aikin samar da zaman lafiya a jihar Delta.

Wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ta fitar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, ta nuna cewa jami’an sun rasa ransu ne a wani harin kwanton ɓauna da ƴan bindiga suka kai musu a dajin Ohoro na jihar Delta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari a Katsina, sun hallaka babban dan siyasa da sace iyalansa

'Yan sandan da aka kashe a Delta
Rundunar 'yan sanda ta saki hotunan 'yan sandan da aka kashe a Delta Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Ƴan sandan dai suna bincike ne a dajin kan ɓacewar wasu abokan aikinsu guda uku lokacin da lamarin ya auku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu jami’an ƴan sandan guda shida kuma sun ɓace bayan an kai musu harin.

Sunayen jami’an da suka rasu

 • Insfeta Abe Olubunmi (IRT), wanda ya fara aiki a ranar 1 ga Agusta 2003
 • Insfeta Friday Irorere (51 PMF), wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu, 2003
 • Sajan Kuden Elisha (51 PMF), wanda ya fara aiki a ranar 17 ga watan Oktoba, 2011
 • Sajan Akpan Aniette (51 PMF), ya fara aiki a ranar 17 ga watan Oktoba, 2011
 • Sajan Ayere Paul (IRT), wanda ya fara aiki a ranar 17 ga watan Oktoba, 2011
 • Sajan Ejemito Friday (51 PMF), ya fara aiki a ranar 17 ga watan Oktoba, 2011

Sunayen jami’an da suka ɓace a wurin aiki

Kara karanta wannan

An samu asarar rayuka bayan 'yan bindigan sun farmaki jami'an 'yan sanda

 • Insfeta Onoja Daniel, ya fara aiki a ranar 1 ga watan Fabrairu 2003
 • Insfeta Onogho Felix, ya fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu 2004
 • Insfeta Emmanuel Okoroafor, ya fara aiki a ranar 1 ga watan Afrilu 2004
 • Insfeta Joel Hamidu, ya fara aiki a ranar 1 ga watan Yuni 2006
 • Sajan Moses Eduvie, wanda aka yi rajista a ranar 17 ga Oktoba 2011
 • Sajan Cyril Okorie (SWAT), ya fara aiki a ranar 17 ga watan Oktoba 2011

IGP ya umurci biyan haƙƙoƙin jami’an da aka kashe

A halin da ake ciki, Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ya bayar da umurnin a gaggauta biyan duk wasu haƙƙoƙin da iyalan jami'an ƴan sanda da suka rasu za su samu.

Ya zuwa yanzu an cafke mutum biyar da ake zargi da hannu a harin.

A cewar rundunar ƴan sandan, a halin yanzu waɗanda ake zargin suna bayar da bayanai domin zaƙulo sauran waɗanda suka aikata laifin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile yunkurin yin garkuwa da mutane a Kaduna

Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu ciki har da wani ɗan siyasa, a wani hari da suka kai a jihar Katsina.

Miyagun ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da mata da ƴaƴa mata biyu na ɗan siyasan a ƙauyen Mairuwa na ƙaramar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel