Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Nada Mace Ta Farko a Mukamin Shugabancin Babbar Hukuma

Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Nada Mace Ta Farko a Mukamin Shugabancin Babbar Hukuma

  • An samu sauyin shugabanci a hukumar yaƙi da yaɗuwar cutar ƙanjamau ta ƙasa (NACA), bayan ƙarewar wa'adin mulkin Dakta Gambo Aliyu
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dakta Temitope Ilori a matsayin sabuwar darakta janar ta hukumar
  • Naɗin na ta ya sanya ta zama mace ta farko a tarihi da ta taɓa riƙe shugabancin hukumar tun bayan da aka kafa ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dakta Temitope Ilori a matsayin sabuwar darakta janar ta hukumar yaƙi da yaɗuwar cutar ƙanjamau ta ƙasa (NACA).

Jaridar The Punch ta ce daraktar hulɗa da jama’a na hukumar ta NACA, Toyin Aderibigbe ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a ranar Alhamis, 13 ga watan Maris 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu ya aike da saƙo majalisa, ya yi sabon muhimmin naɗi a babban bankin Najeriya CBN

Tinubu ya nada shugabar NACA
Shugaba Tinubu nada dakta Temitope Ilori shugabancin hukumar NACA Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Dakta Ilori, wacce ita ce mace ta farko da aka nada a matsayin darakta janar ta hukumar, wa'adin ta na shekara huɗu zai fara ne daga ranar 22 ga watan Fabrairu, 2024, rahoton jaridar Nairametrics ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ilori ta karɓi muƙamin ne daga hannun magabacinta, Dakta Gambo Aliyu, wanda shine shugaban hukumar tun daga watan Yunin 2019 zuwa watan Fabrairun 2024.

NACA: Wacece Dakta Temitope Ilori?

Kafin naɗin da aka yi mata, Dakta Ilori babbar malama ce a sashen nazarin lafiyar al'umma na jami'ar Ibadan.

Sabuwar shugabar hukumar ta NACA, babbar mai bincike wacce ta wallafa rubuce-rubuce da dama kan harkokin kiwon lafiya.

Ta taɓa riƙe muƙamin kwamishiniyar lafiya ta jihar Osun daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2014.

Hakazalika ta taɓa shugabantar hukumar yaƙi da yaɗuwar cutar ƙanjamau ta jihar Osun.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi kudin fansan da gwamnatinsa za ta biya don ceto daliban da aka sace a Kaduna

Tinubu ya nada shugaban NIMASA

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa sabon shugaban hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya (NIMASA).

Shugaban ƙasan ya ɗauko tsohon kwamishina a jihar Legas, Dayo Mobereola, a matsayin wanda zai shugabanci hukumar, biyo bayan ƙarewar wa'adin magabacinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel