Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini a Kokarin Zuwa Binne Mahaifiyarsa, Sun Sace Wasu 15

Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini a Kokarin Zuwa Binne Mahaifiyarsa, Sun Sace Wasu 15

  • An shiga fargaba yayin da wasu ‘yan bindiga suka farmaki motar bas da ke dauke da fasinja a jihar Oyo tare da sace dukkan fasinjojin
  • Maharan yayin harin sun yi garkuwa da wani Fasto kuma shugaban cocin RCCG, Olugbenga Olawore da ke kan hanyarsa ta zuwa Legas
  • Lamarin ya faru da yammacin ranar Juma’a 19 ga watan Afrilu yayin da Faston ke kan hanyarsa domin shirye-shiryen binne mahaifiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo – Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban cocin RCCG, Olugbenga Olawore a jihar Oyo.

Maharan sun sace malamin addinin ne da sauran fasinjojin motar kiras bas a ranar Juma’a 19 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Neja: An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun sake hallaka sojoji tare da sace Kyaftin

Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin addini da wasu fasinjoji
Yan bindiga sun sace Fasto da sauran fasinjoji a cikin bas a jihar Oyo. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Yaushe 'yan bindiga suka sace Faston a Oyo?

Vanguard ta tattaro cewa lamarin ya faru ne yayin da motar bas din ta dauko fasinjoji a cikinta domin zuwa jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 19 ga watan Afriku da misalin karfe 5:00 na yamma a kan hanyar Lanlate zuwa Eruwa.

Faston ya gamu da tsautsayin ne yayin da ya ke dawowa daga Ipapo domin shirye-shiryen gudanar da bikin binne mahaifiyarsa.

Martanin rundunar 'yan sanda kan lamarin

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Osun, SP Adewale Osifeso ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Osifeso ya tabbatar da cewa wasu daga cikin wadanda aka sacen sun samu nasarar kubutar da su.

Ya ce ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro sun durfafi dajin da lmarin ya faru domin ceto wadanda aka sacen, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'Bam' da ƴan ta'adda suka dasa ya halaka bayin Allah sama da 10 a Arewacin Najeriya

“Wasu daga cikin wadanda aka ceton suna taimakawa jami’an tsaro domin yin bincike tare da neman hanyar zuwa cikin dajin.

- Adewale Osifeso

‘Yan bindiga sun hallaka sojoji 6

A wani labarin, kun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun yi ajalin wasu sojoji guda shida a jihar Neja yayin da suka kai musu farmaki.

Yayin harin da ya yi ajalin sojojin a Neja, maharan sun kuma sace wani Kyaftin din soja inda suka tsere da shi zuwa wani wuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel