Kiristan Gwamna Zai Ginawa Musulmai Sansanin Alhazai Na Farko a Jiharsa

Kiristan Gwamna Zai Ginawa Musulmai Sansanin Alhazai Na Farko a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya aza harsashin fara gina katafaren sansanin alhazai, wanda shi ne na farko tun bayan kafa jihar
  • Adeleke ya shaidawa al'ummar Musulmi a jihar cewa zai tabbatar an kammala aikin a kan lokaci domin alhazai su samu gata kamar sauran jihohi
  • Haka zalika, gwamnan ya sha alwashin ba alhazan jihar dukkanin wata gudunmawa da suke bukata a wannan lokaci na tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya aza harsashin ginin sansanin alhazai wa al'ummar Musulmi a jihar.

Gwamna Adeleke ya fara ginin sansanin alhazai a Osun
Za a gina sansanin alhazai na farko a jihar Osun. Hoto: @AAdeleke_01
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa jihar Osun ce kadai jihar da ba ta da sansanin alhazai a Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai mummunan hari a Yobe, sun hallaka soja

An aza harsashin ginin sansanin alhazai

Adeleke yayin wata laccar Ramadan da kungiyar Nasfat ta gudanar a makon da ya gabata ya sha alwashin cewa zai samar da sansanin da zai dace da mahajjata a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka ne, Adeleke a ranar Litinin ya aza harsashin gina sansanin aikin Hajjin bisa rakiyar mataimakinsa, Kola Adewusi, da shugaban al’ummar Musulmin Osun, Sheikh Mustapha Olawuyi.

Sauran manyan baki sun hada da babban limamin Osogbo, Sheikh Musa Animashaun, Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Olanipekun, Timi na Ede, Oba Munirudeen Lawal da sauran shugabannin Musulmi a jihar.

"Alhazai za su ji dadi a Osun" - Adeleke

Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a bayan sakatariyar gwamnati, kamar yadda Radio Nigeria Ibadan ya ruwaito, Adeleke ya ce:

“Me ya sa jihar Osun ce kadai ba ta da sansanin alhazai. Na yi magana a kan hakan makon jiya kuma yau gamu a nan da izinin Allah za mu aza harsashin ginin sansanin.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan PDP na dab da rasa kujerarsa yayin da CJ ya kafa kwamitin mutum 7

“Tun da muka aza harsashin ginin nan take aiki zai fara, domin alhazai su ji dadi a duk lokacin da za su je aikin Hajji, kuma zan taimaka masu a wannan lokaci na tsadar rayuwa."

Gwamna Adeleke ya koma gidan gwamnati

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya koma gidan gwamnati bayan shafe shekara da wanni yana gudanar da mulki daga gidansa.

Tsawon lokacin da ya dauka ba ya aiki a gidan gwamnatin, ya jawo jam'iyyar adawa ta APC a jihar tana yawan sukar gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.