Legas: NASFAT ta tallafawa al'ummar Hausawa a fannin kiwon lafiya
- Kungiyar NASFAT reshen jihar Legas ta tallafawa al'ummar Hausawa mazauna Legas a fannin kiwon lafiya
- Kungiyar ta gudanar da wannan shirin ne tare da haɗin gwiwar kungiyar likitocin Islama ta Najeriya (IMAN)
- Fiye da mutane 400 da yara kanana 270 ne suka amfana da shirin
Kungiyar Nasrul-Lahi-L-Fatih na Najeriya (NASFAT) sashen zakat da sadaqat (NAZAS) za ta gudanar da gwaji a kan kiwon lafiya da kuma ba da magunguna kyauta ga al'ummar Hausawa da ke zaune a yankin Amuwo-Odofin na jihar Legas.
Legit.ng ta tattaro cewa, wannan shirin kiwon lafia ita ce na biyu da aka gudanar a cikin shirin NAZAS kuma an gudanar da ita ne tare da haɗin gwiwar kungiyar likitocin Islama ta Najeriya (IMAN) a Amuwo Odofin, Legas.
Fiye da mutane 400 da yara kanana 270 ne suka amfana da shirin.
KU KARANTA: Gwamnati ta ki cewa komai kan rashin lafiyar Yaron Shugaban kasa
Shugaban IMAN, Dokta Mustapha Alibi wanda kuma shine babban darakta a asibitin ‘National Orthopedic Hospital’, Igbobi ya jagoranci tawagar likitocin tare da wasu kwararrun likitoci 20. NAZAS, wanda aka kafa a shekara ta 2014, ta rarraba fiye da N131.5 miliyan kyauta a matsayin tallafi ga kimani mutane 516.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng