Ahmad Gumi: Hakurin Gwamnatin Tarayya Ya Kare, Ta Dauki Mataki Kan Malamin Musulunci

Ahmad Gumi: Hakurin Gwamnatin Tarayya Ya Kare, Ta Dauki Mataki Kan Malamin Musulunci

  • Yayin da Sheikh Ahmed Gumi ke yawan cece-kuce kan 'yan bindiga, Gwamnatin Tarayya ta gayyace shi kan lamarin
  • Gwamnatin ta dauki matakin ne domin malamin ya masa tambayoyi kan alakarsa da 'yan bindiga a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne yayin da malamin ke sukar tsarin da gwamnati ke bi wurin yaƙi da ta'addanci inda ya bukaci a yi sulhun da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Sheikh Ahmed Gumi domin amsa tambayoyi kan alakarsa da 'yan bindiga.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka a yau Litinin 25 ga watan Maris yayin zantawa da manema labarai, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

2027: Al'ummar Musulmai ba za su taɓa zabar Obi Ba, Reno Omokri ya bayyana dalilai

Matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka kan Gumi
Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Sheikh Gumi domin amsa tambayoyi kan 'yan bindiga. Hoto: Bola Tinubu, Ahmed Gumi.
Asali: Twitter

Wane mataki gwamnati ta ɗauka kan Gumi?

Ministan ya ce babu wanda ya fi karfin doka dalilin haka nema suka gayyaci malamin kan yadda ya ke martani ga ayyukan 'yan bindigan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris ya ce dole Gumi dole ya bi doka kamar sauran 'yan kasa inda ya ce kiran nasa ya na da muhimmanci domin amsa wasu tambayoyi, cewar TheCable.

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin ta gaji da yadda shehin malamin kuma tsohon soja yake shiga harkar yaki da ta'addanci a Najeriya.

Yadda Gumi yake martani kan 'yan bindiga

Idan ba a manta ba, Gumi ya na yawan magana kan yadda ya kamata a bi da maharan domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Har ila yau, malamin ya ce a shirye ya ke ya jagoranci yin sulhu da 'yan ta'addan idan bukatar hakan ta taso.

Kara karanta wannan

Abacha ya karkatar da maƙudan kudi a mulkinsa? Buba Galadima ya fayyace gaskiya

Gumi ya shawarci Tinubu kan yin sulhun inda ya gargade shi da kada ya yi kuskure irin na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

"Yadda 'yan ta'adda ke samun kuɗi" - Gumi

Kun ji cewa Sheikh Ahmed Gumi ya ƙaryata cewa wasu na daukar nauyin ta'addanci a Najeriya kamar yadda gwamnati ta fitar.

Shehin malamin ya ce babu wanda ke da ikon ayyana wani a matsayin mai daukar nauyin ta'addanci sai kotun shari'a.

Ya ce babu wani ɗan Najeriya da zai ɗauki maƙudan kuɗi na biliyoyin naira domin ɗaukar nauyin ta'addanci a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel