Google Ya Horar Dalibai kan Fasahohin Zamani a Jami’ar YSU a Arewacin Najeriya

Google Ya Horar Dalibai kan Fasahohin Zamani a Jami’ar YSU a Arewacin Najeriya

  • Kamfanin Google ya hada kai da kwararru wajen horas da daliban da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya
  • An zabi wannan shiyya ne ganin yadda aka bar su a baya musamman bayan rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram
  • Jami’ar jihar Yobe tana cikin wadanda suka samu wannan dama, dalibai 50 suka amfana da tsarin ExploreCSR
  • Legit ta zanta da Bashir Saleh Maina wanda shi ne shugaban wannan shiri da aka kawo a jami'ar da ke Damaturu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Yobe - Kamfanin Google ya dauki dawainiyar horar da daliban da ke karatu a wasu jami'o’i da ke Arewacin Najeriya.

Legit ta samu labarin yadda wasu jamio’in da ke Arewa maso gabas suka amfana da wani tsari mai suna ExploreCSR.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai mummunan hari a Yobe, sun hallaka soja

Taron ExploreCSR
Taron ExploreCSR da Google suka shirya a a kan AI a Jami'ar YSU a Yobe Hoto: Bashir Maina
Asali: Facebook

AI: Google sun kawo shirin ExploreCSR

Jami’ar jihar Yobe da ke garin Damaturu tana cikin wadanda suka amfana da tsarin na Google, an horar da dalibai 50.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanan da aka samu daga YSU sun nuna, Google ya fito da exploreCSR domin taimakawa wadanda aka bari a baya.

Google ya taimakawa Arewa maso gabas

Kamfanin na Google ya bada fifiko a kan Arewa maso gabashin Najeriya inda aka yi masu nisa wajen ilmin zamani.

An yi wannan horo na tsawon kwanaki biyar ne daga 5 ga watan Maris 2024 a kan bangarorin fasahar AI da ML a YSU.

An zakuko daliban da aka ba horo daga masu digirin farko zuwa manyan digirori a jami'ar Yobe a fannin ilmin komfuta.

A shekarar nan, jami’ar jihar Yobe tana cikin makarantu shida da aka zaba a Najeriya, kuma an halarta har ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

Mun tada matattu sama da 50 a cocina bayan tabbatar da mutuwarsu, inji malamin coci Chris

Manufar shirin ExploreCSR a Yobe

Jagoran wannan shiri, Bashir Saleh Maina ya ce sun dauko kwararru daga fadin kasar domin ilmantar da daliban nasu.

Bashir Maina ya fadawa Legit cewa burinsu shi ne tallafawa daliban Arewa maso gabas wajen ganin sun kware a harkar AI.

"Burinmu shi ne a yi amfani da tallafin domin taimakawa daliban Arewa maso gabashin Najeriya wajen harkar bincike a kan AI."

- Bashir Saleh Maina

Malamin ya ce an yi zama iri-iri, an ba da ayyuka bayan makaloli da masana suka gabatar da nufin bunkasa ilmin AI a yankin.

Shirin gwamnonin Arewa a Ramadan

Idan aka bar batun kimiyya, ana da labari akalla Gwamnonin Arewa bakwai suka kaddamar da shirin ciyarwa a Ramadan

A yayin da jihar Katsina ta fitar da N10b domin aiwatar da shirin, Yobe ta kashe N187m, irinsu Kano za su batar da N1.19bn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel