Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Gano Babban Dalilin da Yasa Ake Samun Rashin Tsaro a Arewa

Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Gano Babban Dalilin da Yasa Ake Samun Rashin Tsaro a Arewa

  • Gwamonin Arewa maso Gabas sun koka kan yadda rashin tituna masu kyau ke zama barazana ga zaman lafiya a yankin
  • Sun kuma bayyana matsalar gurbacewar muhalli daga cikin matsalolin da jihohin Arewa maso Gabas ke fuskanta
  • Yankin ya sha fuskantar matsalolin tsaro, ciki har da na Boko Haram da ISWAP da aka samu a shekarun baya-bayan nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Adamawa - Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta ce lalacewar tituna na haifar da rashin tsaro da dakile ci gaba tare da kara jefa al’ummar yankin cikin mawuyacin hali, TheCable ta ruwaito.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da aka fitar a karshen taro karo na tara da shugaban kungiyar, Gwamna Babagana Zulum na Borno ya sanyawa hannu a Yola ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi umurnin nada mataimakin Akeredolu a matsayin mukaddashin gwamna? Gaskiya ta bayyana

Gwamnoni sun koka kan yadda tituna suka lalace a Arewa
Lalacewar tituna na daga tushen matsalar tsaro a Arewa | Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Halin da titunan Arewa maso Gabas ke ciki

Wani yankin sanarwar ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Abin damuwa yadda aka yi watsi da titunan gwamnatin tarayya a ciki da tsakanin jihohin yankin.
"Don haka, kungiyar na kira ga ma'aikatar ayyuka ta tarayya da ta bi diddigin kwangilar hanyoyin da aka bayar a yankin."

Taron ya yi nuni da cewa yanayin tsaro yana kara inganta a yankin tare da bayyana bukatar kara hada kai a tsakanin jihohin yankin wajen tsara hanyoyin magance tsaro.

Wata sabuwar matsalar Arewa maso Gabas

An kuma ruwaito cewa, gwamnonin sun lura da sauyin yanayi da gurbacewar muhalli har yanzu batutuwa ne masu girma da suka shafi yankin, rahoton Daily Nigerian.

A cewar sanarwar, gwamnonin sun kuduri aniyar karfafa hadin gwiwa tare da kawo duk wasu tsare-tsaren da za su zama mafita ga yankin na Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Miji ya zargi surukinsa hakimi, basarake a Kano da kashe masa aure tare da yunkurin tozarta shi

Arewa maso Gabas ne yankin da ya sha fama da barnar Boko Haram da ISWAP a shekarun da suka gabata.

Rarara ya gina tituna a jiharsa

Dauda Adamu Abdullahi, wanda aka fi sani da Kahutu Rarara ya ba da aikin gina tituna guda bakwai a wasu yankunan jihar Katsina.

Wannan na fitowa ne daga bakin mai magana da yawunsa Rabi’u Gabra Gaya a lokacin da ya yada wasu hotunan aikin titi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 10 Satumba, 2023.

A hotunan, an ga motocin kankare da ke sharbar kasa a kokarin yin aikin titi wani yankin da Gaya yace ana aikin ne a jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel