Gwamna Abba Ya Karyata Masu Jita-Jita Cewa Ya Ware N6bn Don Ciyar da Kanawa a Ramadana

Gwamna Abba Ya Karyata Masu Jita-Jita Cewa Ya Ware N6bn Don Ciyar da Kanawa a Ramadana

  • Gwamnan Kano ya bayyana gaskiyar kudin da ya ware don ciyar da al'ummar jihar a cikin watan Ramadana
  • Ya shawarci 'yan jarida da su daina yada labaran da basu tabbatar ba, inda ya bayyana bacin ransa kan hakan
  • An fara rabon abincin buda-baki a Kano, gwamna bai ji dadi ba bayan ganin kalan abincin da ake girkawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya musanta rahotannin da aka yada cewa gwamnatinsa ta ware Naira biliyan 6 don ciyar da mutane a watan Ramadana.

Gwamnan ya bayyana wannan batu ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Lahadi 24 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

N6bn: 'Yan APC a Kano sun taso Gwamna Abba a gaba kan kudaden ciyar da bayin Allah a Ramadana

Abba ya bayyana kudin da yake kashewa wajen ciyar da jama'a a Ramadana
An fadi kudin da ake kashewa a Ramada a Kano | Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Idan baku manta ba, ganin yawan kudin da aka ce Abba ya ware ya sa APC ta fara zargin lauje cikin nadi a harkar ciyarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya fadi kudin da ake kashewa

Sai dai, da yake ba da bahasi kan lamarin, Abba ya rubuta cewa:

“A ‘yan kwanakin da suka gabata, na lura da yadda kafafen yada labarai ke ta yada jita-jita game da gwamnatinmu wai mun kasafta Naira biliyan 6 don ciyar da mutane a watan Ramadan.
"Ina so in bayyana karara cewa ainihin kudin da ake kashewa a shirin shine jimillar Naira biliyan daya da miliyan dari da casa’in da bakwai da dubu dari bakwai, na tsawon wata guda.
"Ina kuma shawartar 'yan jarida da su tabbatar da cewa sun samu alkalumansu daidai game da ayyukanmu daga majiyoyin da suka dace don gujewa yada alkaluman bogi."

Kara karanta wannan

Mun tada matattu sama da 50 a cocina bayan tabbatar da mutuwarsu, inji malamin coci Chris

Abba ya fusata bayan ganin abincin da ake rabawa

Gwamnan, a ranar Juma’a, ya bayyana bacin ransa game da yadda shirin ciyarwar ke tafiya a jihar ta Kano da ke Arewa maso Yamma.

Ya bayyana rashin jin dadinsa ne a lokacin da ya kai ziyarar bazata a inda ake rabon abincin da ke Gidan Maza, a Kano ta Tsakiya.

Abba ya soki masu kula da shirin kan yadda aka jirkita yanayin abincin da kuma raba shi ga wadanda ba su aka niyyar rabawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel