Tsohon Gwamnan PDP ya shiga uku, EFCC ta gabatar da hujjar ya saci Biliyan 9.7

Tsohon Gwamnan PDP ya shiga uku, EFCC ta gabatar da hujjar ya saci Biliyan 9.7

- EFCC ta kira Abubakar Umar ya bada shaida a shari’ar da ta ke yi da Mr Gabriel Suswam

- Umar ya ce ya damkawa tsohon gwamnan na Benuwai $15.8m a wani gidansa a Abuja

- A baya wannan Bawan Allah ya canza maganar da ya yi wa EFCC saboda matsin-lamba

Abubakar Umar, wani wanda hukumar EFCC ta kira ya bada shaida a gaban kotu, ya fadi yadda ya ba Sanata Gabriel Suswam kudi fam dala miliyan 15.8.

Mista Abubakar Umar ya tabbatar da cewa ya mika wa tsohon gwamnan na jihar Benuwai wannan kudi ne a gidansa da ke unguwar Maitama, Abuja.

Hukumar EFCC ta bayyana wannan a wani jawabi da ta fitar a ranar Laraba, 24 ga watan Maris, 2021.

KU KARANTA: Jerin wadanda su ka rike mukamin shugaban hukumar EFCC

EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta ce Umar ya yi wannan da’awa, amma daga baya, sai ya dawo ya canza magana.

Wannan Bawan Allah ya canza magana ne saboda barazanar da ya fuskanata daga wurin ‘mutanen Suswam’, wanda ake zargi da laifin satar Naira biliyan 9.7.

Umar yake cewa an bukaci ya canza shaidar da ya bada a game da wanda ya mika wa wannan makudan dalolin kudi da kuma inda wannan lamarin ya faru.

Shaidan na EFCC ya ce wata rana a 2014, Suswam ya kira shi gidansa a Maitama, ya gabatar masa da wata mata, ya fada mata ta ba shi lambar asusun bankinta.

KU KARANTA: An yi watsi da tuhumar da ake yi wa Yari na satar N900bn

Tsohon Gwamnan PDP ya shiga uku, EFCC ta gabatar da hujjar ya saci Biliyan 9.7
Sanata Gabriel Suswam
Asali: Facebook

Umar yake cewa: “Suswam ya ce idan na samu kudin, in ba shi su a Dala, kuma haka na yi. Kudin sun kai fam $15.8m, a lokacin an yi canjin Dalar a kan 197.”

“Na mika wa Suswam ruwan kudin a Dala a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.” Inji shaidan

Alkali ya dakatar da shari’ar zuwa ranar Talata, 25 ga watan Mayu, 2021, domin a cigaba da sauraron karar tsohon gwamnan da wani kwamishinansa.

Ku na da labari cewa Najeriya ta karbo wasu daga cikin kudin da tsohon gwamnan Delta, James Ibori, ya sace, amma ana korafi bayan ta zabi ta zauna a kansu.

Gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa ya aika takarda a kan kudin ‘jihar Delta’ da gwamnatin tarayya ta karbe bayan an karbo daga Birtaniyya.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng