Malamin Addini Ya Roki Gwamnan Arewa Ya Ba Murja Kunya Mukamin Hadima a Gwamnatinsa

Malamin Addini Ya Roki Gwamnan Arewa Ya Ba Murja Kunya Mukamin Hadima a Gwamnatinsa

  • Sheikh Ibrahim Khalil, babban malamin addini a jihar Kano, ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya ba Murja Kunya muƙamin 'SSA' ko 'SA'
  • A cewar Khalil, idan aka ba Murja wannan mukami musamman na bangaren kafofin sada zumunta, za ta bunkasa rayuwar matasan jihar
  • Malamin addinin ya ce kuskure ne a daure Murja domin hakan ba zai shiryar da ita ba, amma ba ta mukami zai iya canja rayuwarta gaba daya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Babban malamin addinin Muslunci a jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya ba Murja Kunya muƙamin hadimarsa ta fuskar kafofin sada zumunta.

Kara karanta wannan

Yadda za a bi a maido Dalar Amurka N160 daga N1600 Inji Masanin tattalin arziki

Malamin addinin ya ce yin hakan zai kawo karshen nuna rashin kunya da ake ganin Murja na yi, kuma zai bude kofar kawo sauyi a rayuwar masu amfani da kafofin sada zumunta.

An roki Abba ya ba Murja mukami a Kano
Sheikh Ibrahim Khalil ya nuna wa Gwamna Abba alfanun ba Murja mukami. Hoto: Murja Ibrahim Kunya
Asali: Facebook

A wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo na Freedom Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina kira ga mai girma gwamna da ya ba 'yata Murja Kunya muƙamin SSA, ko S.A, ko P.A na 'social media' ta yadda za ta koya wa mata yadda za su ci ribar amfani da kafofin sada zumunta."

"Daure Murja ba mafita bane" - Ibrahim Khalil

Sheikh Khalil ya yi nuni da cewa akwai wadanda ba su san addini ba da za su iya sukar wannan bukatar ta sa, "amma ba za mu biye wa irin wadannan marasa kan gadon ba."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

"Mu dai muna kira ga gwamna da ya ba Murja SA ko SSA, domin zai taimaki 'yan Kano, hukumar Hisbah da gwamnatin Kano."

- A cewar Sheikh Ibrahim Khalil.

Sheikh Khalil ya ce daure Murja ba zai kawo maslaha a abubuwan da take yi, kuma hakan zai kara tunzura ta ne tare da kawo hankalin masu kare hakkin bil' Adama su saka baki a lamarin.

"Murja za ta canja rayuwar matasa" - Khalil

Ya ce idan har aka ba Murja wannan mukami, za a samu kwanciyar hankali tare da dakile lalatattun mutane daga amfani da ita wajen cimma wata muguwar manufa tasu.

"Ba daidai ba ne kiran ta lalatacciya, ko 'yar iska da sauransu. Kowa ya san tana da mabiya da yawa, kenan akwai bukatar amfani da ita wajen wayar da kan mutane muhimmancin kafofin sada zumunta.
"Malami na iya shekara goma yana huduba a kan wani abu da ya shafi sada zumunta, amma ita Murja a rana daya tana iya warware maka wannan mas'alar tun da ana bibiyarta a harkar."

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ambasada Bawa ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, bayanai sun fito

- Ibrahim Khalil

Malamin ya kuma ce akwai bukatar a hada Murja da wata Hafsa Adama domin yin taimakekeniya wajen wayar da kan matasa.

Kalli bidiyon a kasa:

Abubuwa 5 game da shari'ar Murja

Tun bayan da rahoton kama Murja Ibrahim Kunya ya karade kafofin sada zumunta, mutane suke tofa albarkacin bakinsu, har zuwa kai ta kotu da labarin fitar da ita zuwa gwajin kwakwalwa.

Legit Hausa ta bibiyi yadda shari'ar shahararriyar 'yar TikTok din ya kasance, tare da tattaro maku wasu muhimman abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da shari'ar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel