Majalisar Dattawa Ta Bankaɗo Kura-Kurai a Bashin N30tn da CBN Ya Ba Gwamnatin Buhari

Majalisar Dattawa Ta Bankaɗo Kura-Kurai a Bashin N30tn da CBN Ya Ba Gwamnatin Buhari

  • Majalisar dattawa ta ce ta bankado kura-kurai a bashin N30tn da bankin CBN ya ba gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari
  • Wannan bincike ya sa majalisar ta gayyaci gwamnan CBN, Olayemi Cardoso domin ya bayar da bahasi na yadda aka samu kura-kuran
  • Majalisar ta kuma yi bayani kan binciken shirin Anchor Borrowers da take yi, wanda ta ce ta gano an kammala kaso 70% na shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja -Majalisar dattawa ta ce ta bankado wasu kura-kurai da aka tafka a lokacin da tsohon shugaban kasar ya karbi bashin N30tn a wajen bankin CBN.

Majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan CBN, Olayemi Cardoso
Majalisar dattawa ta gano kuskure a a bashin N30tn da CBN ya ba gwamnatin Buhari. Hoto: @NGRSenate,@DrYemiCardoso
Asali: UGC

The Punch ta ruwaito cewa kwamitin wucin gadi na majalisar da ke binciken yadda aka kashe kudin lamunin 'Ways and Means' ne ya bankado wadannan kura-kurai.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya sake cin karo da babbar matsala kan takarar da yake nema karo na 2

"CBN ya ba Buhari bashin N30tn" - Jibrin

Sakamakon wannan bincike, kwamitin ya ce ya kammala shirin gayyatar gwamnan CBN na yanzu, Olayemi Cardoso, domin ya yi bayani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa bayan da shugaban kwamitin, Sanata Isah Jibrin (Kogi ta Gabas) ya gana da wakilan CBN a majalisar a ranar Talata.

Mataimakin gwamnan babban bankin, Bala Bello ne ya jagoranci tawagar CBN zuwa majalisar, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Sanata Jibrin ya yi zargin cewa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya sa hannu wajen bayar da basussuka ba tare da bin ka'ida ba.

CBN: Binciken majalisa kan shirin Anchor Borrowers

A cewar shugaban kwamitin, Emefiele bai nemi shawarar daraktocin CBN wajen sa hannu a bayar da basussukan ba, wanda ya saba dokar bankin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamitin ya kuma yi tsokaci kan binciken da yake yi a kan shirin bayar da lamuni ga manoma na Anchor Borrowers.

Kara karanta wannan

Malaman jami'a karkashin SSANU za su shiga yajin aiki, sun fadi yaushe za su dawo

Ya ce tsohuwar gwamnatin Buhari da CBN sun aiwatar da kaso 70% na shirin yayin da aka yi watsi da kaso 30%.

Haka zalika, Sanatan ya ce idan har gwamnan CBN na yanzu ya gaza kare kansa kan binciken kwamitin, za su gayyato Emefiele domin ya bayar da bahasi.

Bankin CBN ya tsaida ba gwamnati bashi

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya sanar da cewa ya dakatar da ba gwamnati bashin kudi har sai ta biya wanda take binta yanzu.

Gwamnan bankin, Olayemi Cardoso ya bayyana hakan yana mai cewa CBN na bin gwamnati bashin N4.36tn na 'Ways and Means' wanda ya zarce ka'idar bankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.