Malaman Jami’a Karkashin SSANU Za Su Shiga Yajin Aiki, Sun Fadi Yaushe Za Su Dawo

Malaman Jami’a Karkashin SSANU Za Su Shiga Yajin Aiki, Sun Fadi Yaushe Za Su Dawo

  • Kungiyar malaman jami'a ta SSANU ta bayyana shiga yajin aiki a ranar Litinin mai zuwa, 18 ga watan Maris
  • Wannan na zuwa ne bayan da gwamnati ta ki biya musu bukatunsu na tsawon shekaru ya zuwa yanzu
  • Har yanzu ana ci gaba da kai ruwa rana da malaman jami'a game da kudaden da ya kamata a biya su a matsayin malamai

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kano - Kungiyar manyan malaman jami'a a Najeriya (SSANU) za ta shiga yajin aikin kwanaki bakwai na gargadi daga ranar Litinin 18 ga watan Maris.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta gaza biyawa malaman bukatunsu da suka gabatar a baya.

Kara karanta wannan

Bayan rage farashin abinci, Gwamnan APC ya lissafo kasuwannin da za a iya samun kayan cikin sauki

Daily Trust ta ruwaito cewa, kadan daga abin da ya tunzura su zuwa yajin aikin akwai batun da ya shafi waiwaye ga yarjejeniyarsu da gwamnati a shekara ta 2009.

Za a fara yajin aikin SSANU ranar Litinin
Ranar Litinin za a fara yajin aikin SSANU | Hoto: @SSANU_NATIONAL
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meye yarjejeniyar ke kunshe da ita?

Wannan yarjejeniya dai na kunshe da bukatar karin kaso 25%/35% na albashi, inganta mafi karancin albashinsu da kuma batun N50bn da gwamnatin ta yi alkawarin ba su da sunan alawus.

Da yake zantawa da Daily Trust, shugaban kungiyar na jami'ar BUK a Kano, Mustapha Aminu ya bayyana cewa, gamayyar kungiyar ta amince da a tafi yajin aikin.

Matsayar malaman SSANU

A cewar shugaban na SSANU a Kano:

“Taron na daga cikin umarnin hukumar ta kasa cewa ya kamata mu kira taron gaggawa saboda za mu fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai daga ranar 18 ga wannan wata, kuma yanzu za ka ga kusan kowa na goyon bayan wannan yajin aiki don haka tabbas ba za mu sarara ba.

Kara karanta wannan

Jerin sanatoci 13 na majalisar dattawa ta 10 da suka taba riƙe muƙamin gwamna

“Ya zuwa ranar 18 ga watan Maris idan gwamnati ba ta ce komai ba to mun riga mun shiga yajin aikin kenan.
“Kamar yadda a halin yanzu gwamnati ba ta yi komai ba don haka muna jiran gwamnati ta mayar da martani idan ba haka ba kuma, to yaren da suke fahimta shi ne yajin aiki kuma a shirye muke mu shiga.
"Bayan yajin aikin gargadi na kwana bakwai, za mu shiga yajin aikin sai baba ta gani."

Daga nan ne ya bayyana cewa, babu wani mamba na kungiyar da zai ki shiga yajin aiki, kuma ba za su fito aiki a jami'o'i ba.

Yadda tun farko suka so shiga yajin aiki

A tun farko kun ji cewa, kungiyoyin ma'aikatan Jami'o'i na NASU da SSANU za su tsunduma yajin aikin gargadi.

Kungiyoyin sun sanar da yajin aikin ne na kwanaki bakwai daga ranar 18 ga watan Maris kan rike masu albashi.

Kungiyar ta tabbatar da shirin shiga yajin aikin ne kan albashin ma'aikatan su da aka rike na watannin hudu, cewar Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel