Babban Labari: CBN Ya Dakatar da Ba Gwamnatin Tarayya Bashi Saboda Dalili 1 Tak

Babban Labari: CBN Ya Dakatar da Ba Gwamnatin Tarayya Bashi Saboda Dalili 1 Tak

  • Babban bankin Najeriya ya ce daga yanzu ba zai kara ba gwamnatin tarayya bashin kudi a tsarin lamuni na 'Ways and Means' ba
  • Gwamnan babban bankin, Olayemi Cardoso ya ce CBN na bin gwamnti bashin naira tiriliyan 4.36 wanda ya saba wasu dokokin bankin
  • A cewar Cardoso, har sai gwamnatin ta biya wadannan kudaden ne bankin zai iya ci gaba da bata wasu basussukan a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce daga yanzu ya daina bayar da bashin 'Ways and Means' ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Gwamnan babban bankin na CBN, Olayemi Cardoso, ya ce ya dauki matakin ne saboda gazawar gwamnati wajen biyan basussukan da ake bin ta.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon APC ya gaji da tsarin Tinubu, ya nemi a sake zama kan tsare-tsaren gwamnati

CBN ya dakatar da ba gwamnatin tarayya bashi.
Gwamnan bankin CBN, Mr Cardoso ya dakatar da ba gwamnatin tarayya bashi. Hoto: @DrYemiCardoso
Asali: Twitter

Cardoso ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wani zaman tattaunawa da kwamitin majalisar dattawa kan harkokin banki, inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta kure adadin kudin da CBN zai iya bata

Akwai ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Olawale Edun, ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Atiku Bagudu da kuma ministan noma, Abubakar Kyari a wajen taron.

'Ways and Means' wani lamuni ne da CBN ke bai wa gwamnatin tarayya don cike duk wani gibin kudi da aka samu a kasafin kudi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An dai tabka cece-ku-ce akan ba da lamunin, inda masana ke nuna damuwarsu kan yadda CBN ya zarce matakin ba da lamuni ga gwamnatin tarayya bisa wasu dokoki.

Bashin da gwamnatin tarayya ta samu daga bankin CBN ya kai naira tiriliyan 4.36 a watan Yunin 2023, wata daya bayan da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ciyo bashin naira tiriliyan 22.7 daga bankin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya zage yayi karin albashi, ma’aikatan Jihar sun raina N10, 000 a wata 3

Adadin bashin da yanzu CBN ke bin gwamnatin Najeriya

Yanzu ana bin gwamnati bashin naira tiriliyan 4.36 wanda ya zarce kashi biyar cikin dari na kudaden shigar gwamnatin tarayya na naira tiriliyan 8.8 na shekarar 2023 wanda ya sabawa dokar CBN.

Tsakanin watan Yuli zuwa Disamba 2023, gwamnatin tarayya ta shiga lalitar babban bankin na CBN ta karbi kudi har naira tiriliyan 2.94.

A watan Disamba na shekarar 2023, majalisar ta amince da bukatar shugaban kasa na bai wa gwamnatin tarayya karbar naira tiriliyan 7.3 daga wajen CBN.

Gwamnan babban bankin a yanzu ya ce bashin da ake ba gwamnatin tarayya zai tsaya har sai an biya na baya. Wannan matakin, in ji Cardoso, ya bi umurnin sashe na (38) na dokar CBN (2007).

Majalisa ta amince Tinubu ya ciwo bashin dala biliyan 7.8

A wani labarin kuma, Legit ta ruwaito maku cewa majalisar dattawa ta amince shugaban kasa Tinubu ya karbo bashin dala biliyan 7.7.

A lokacin da ya mika bukatar ciyo bashin, Tinubu ya sanar da cewa zai yi amfani da kudin ne don kammala wasu ayyukan raya kasa da aka fara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel