Ana bin Najeriya Naira Tiriliyan 33, kowane ‘dan kasa na da bashin N175, 000 a kansa

Ana bin Najeriya Naira Tiriliyan 33, kowane ‘dan kasa na da bashin N175, 000 a kansa

  • DMO yace tulin bashin da ake bin gwamnatocin Najeriya ya karu da N2.36tr
  • Ofishin tattara bashin yace gwamnatin tarayya ta ke dauke da 83% na kason
  • Kasashen da suke bin Najeriya bashi sun hada da Sin, Faransa har da Indiya

Abuja - Ofishin da ke kula da bashin Najeriya yace adadin kudin da ake bin gwamnatocin jihohi da na tarayya a tsakiyar 2021 ya doshi N35.46tr.

The Cable tace hakan na nufin an samu karin N2.36tr idan aka kamanta da alkaluman da aka fitar a karshen Maris, lokacin da aka tsaya a kan N33.10tr.

Darekta-Janar na DMO, Patience Oniha, ta bada adadin kudin da ake bin kasar a lokacin da ta yi wa ‘yan jarida jawabi a ranar 15 ga watan Satumba.

Patience Oniha tace gwamnatin tarayya ke dauke da 83.07% na bashin da ke kan kasar. Gwamnatocin jihohi da birnin tarayya sun dauki 16.93%.

Kara karanta wannan

NDLEA sun yi nasarar dakile kilogram 24, 311 na Koken, Codeine da kwayoyi da za a shigo da su

An rahoto Oniha tana cewa adadin kudin da aka aro daga kasar waje ya tashi da N12.47tr a watan Maris zuwa N13.71 a karshen watan Yuni, karin 9.94%.

Shugaban Najeriya
Shugaba Buhari zai hau jirgin sama Hoto: www.nigerianeye.com
Asali: UGC

Haka zalika kudin da aka karbi aro a cikin gida sun karu daga N20.64tr a Maris zuwa N21.75 a karshen watan Yuni, adadin bashin ya karu da N1.11tr.

Daily Trust ta rahoto Darektar ta DMO tana cewa suna neman umarni daga gwamnatin tarayya domin a canza salon yadda za a biya wasu bashin CBN.

A ina Najeriya ta fi cin bashi?

Wadanda suke kan gaba wajen ba gwamnatin Najeriya aron kudi a ketare sune Babban bankin Duniya da kuma African Development Group da 54.88%

Bayan haka ofishin DMO yace 12.70% na bashin da Najeriya ta karbo daga kasashen waje sun fito ne daga kasashen Sin, Jafan, Faransa, Jamus da Indiya.

Kara karanta wannan

Bincike: Akwai bindigogi AK-47 sama da 60,000 a sansanonin 'yan bindiga 120

Ana hasashen cewa akwai mutane kimanin miliyan 200 a Najeriya. Hakan yana nufin kowane ‘dan kasar nan yana da bashin N175, 000 a kansa a halin yanzu.

Meyasa Buhari ya gane wa bashi?

Ganin gwamnati na neman wani bashi ne aka ji Jam’iyyar APC ta fito tana cewa Muhammadu Buhari yana karbo bashi ne domin ayi wa al'umma ayyuka.

Idan aka kamanta adadin bashin da karfin tattalin arzikin arzikin kasa, ya koma 21.92% a yanzu. Da wannan gwamnati ta ke kafa hujja, tana sake aro kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel