Majalisar Dattawa Ta Kaddamar da Kwamitin Binciken Lamunin N30trn Na CBN da Buhari Ya Karba

Majalisar Dattawa Ta Kaddamar da Kwamitin Binciken Lamunin N30trn Na CBN da Buhari Ya Karba

  • Majalisar dattawa ta kaddamar da kwamiti wanda zai binciki gwamnatin Buhari kan yadda ta batar da N30trn na aron 'Ways and means'
  • Lamunin 'Ways and Means' wani bashin kudi ne wanda bankin CBN yake ba gwamnati domin cike gibi cikin kasafin kudin gwamnati
  • Haka kuma, majalisar ta ba kwamitin umarnin gudanar da bincike kan shirin ba manoma rancen kudi na a tsarin 'Anchor Borrowers’

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A ranar Litinin ne majalisar dattawa ta kaddamar da kwamitin da zai binciki yadda aka batar da Naira tiriliyan 30 na lamunin 'Ways and Means' da bankin CBN ya ba gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba gwamnonin jihohi sabon umarni kan mafi karancin albashi, bayanai sun fito

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamitin yana da alhakin gudanar da bincike kan shirin bashin manoma wanda gwamnatin Buhari ta aiwatar.

Majalisa na tuhumar gwamnatin Muhammadu Buhari
Majalisar dattawa ta kafa kwamiti na bincikar gwamnatin Buhari. Hoto: @SPNigeria, @MBuhari
Asali: Twitter

Legit Hausa ta ruwaito cewa lamunin wani bashin kudi ne wanda CBN ke ba gwamnati domin cike gibin kasafin kudin gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken kwamitin yana da muhimmanci - Akpabio

Kaddamar da kwamitin ya biyo bayan wani rahoto da kwamitocin hadin gwiwa kan harkokin banki, inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi na majalisar suka gabatar.

The Cable ta ruwaito cewa sauran cibiyoyin sun hada da; bangaren kudi, tsare-tsaren kasa; noma da kuma na kasafi.

An kuma kafa kwamitin bayan doguwar ganawa da tawagar gwamnatin tarayya da ke kula da tattalin arziki.

Da yake jawabi yayin taron a Abuja, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce kwamitin binciken na da “muhimmanci domin gano yadda aka yi da kudadaden."

Kara karanta wannan

Duk da gwamnati ta dauki mataki, farashin gas din girki ya sake lulawa har ya haura N1300

Majalisa ta fara tuhumar gwamnatin Buhari

A hannu daya kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar wakilai, ta kafa kwamiti da zai binciki gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari kan naira biliyan 200 da ta kashe a shirin kidayar 2023.

Idan ba a manta ba, hukumar kidaya ta kasa, ta ce ta kashe akalla naira biliyan 200 a shirin kidayar mutane da gidaje, amma ta sanar da dage shirin saboda zabubbukan wasu jihohi.

Sai dai ana kwanaki kadan ya sauka daga kan mulki, Muhammadu Buhari ya sanar da dage shirin kidayar har sai baba-ta-gani, lamarin ya jawo cece uce kan kudin da aka kashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel