Gwamnan APC Ya Sake Cin Karo da Babbar Matsala Kan Takarar da Yake Nema Karo Na 2

Gwamnan APC Ya Sake Cin Karo da Babbar Matsala Kan Takarar da Yake Nema Karo Na 2

  • Jigon jam'iyyar APC a jihar Ondo, Sola Olatunji ya bukaci Gwamna Lucky Aiyedatiwa da ya janye takarar da ya ke son nema
  • Olatunji ya ce tsayawa takarar gwamnan a yanzu zai dakile muradin al'ummar yankin Ondo ta Kudu na yin shekaru takwas a mulki
  • Ya kuma gargade shi da ka da ya kuskura ya biyewa son ransa domin lalata farin cikin al'ummar yankin kan wannan zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar Ondo, jigon jam'iyyar APC ya ba Gwamna Lucky Aiyedatiwa shawara kan takara.

Sola Olatunji ya bukaci gwamnan da ya janye takararsa saboda kada ya rage wa'adin da Kudancin jihar za su yi, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Kabir ya ware maƙudan kuɗi domin ciyar da mabuƙata a watan Ramadan

Gwamnan APC ya fara cin karo da matsala kan takarar da ya ke nema karo na biyu
Jigon APC Ya Ba Gwamna Lucky Na Ondo Shawara Kan Sake Tsayawa Takara. Hoto: Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Menene jigon APC ke cewa kan Gwamna?

Olatunji wanda ya fito daga yankin Erekiti a karamar hukumar Okitipupa ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Talata 19 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon APC ya ce idan Gwamna Lucky ya tsaya takara kuma ya yi nasara, ta tabbata ba zai sake tsayawa takara ba a wa'adi na biyu kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ce hakan zai dakile muradin yankin Kudancin jihar domin samun damar yin shekaru takwas a kan mulki kamar sauran yankuna, cewar New Telegraph.

Shawarar da jigon APC ya ba gwamnan

"Akwai bambanci karara tsakanin shekaru takwas da kuma hudu, rashin imani ne mutum ya biyewa son ransa tare da lalata farin cikin wasu."
Sauran yankuna kamar Arewaci da kuma Ondo ta Tsakiya duk sun yi shekaru takwas a kan mulki, wannan lokacin 'yan Kudancin jihar ne suyi shekaru takwas su ma."

Kara karanta wannan

Ramadan: Dan takara a PDP ya gwangwaje shugabannin jam’iyyar da N7.8m

"Saboda muradin 'yan Kudancin jihar, dole gwamnan ya janye takararsa domin gujewa zanga-zanga daga al'ummar yankin Ondo ta Kudu."

- Sola Olatunji

Betty Akeredolu ta soki surukarta kan siyasa

Kun ji cewa matar marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ta caccaki surukarta kan goyon bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa.

Betty Akeredolu ta soki Funke Akeredolu ne saboda ta fito karara ta na nuna goton baya ga gwamnan jihar na yanzu.

Ta ce bata taba ganin mace butulu irinta ba bayan ta gama cin duniyarta a mulkin marigayin tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel