Kisan Sojoji 16: Majalisar Dattawa Ta Dauki Muhimmin Mataki

Kisan Sojoji 16: Majalisar Dattawa Ta Dauki Muhimmin Mataki

  • Majalisar dattawan Najeriya ta bada umurnin gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa sojoji 16 a jihar Delta
  • Majalisar ta cimma wannan matsayar ne biyo bayan ƙudirin da Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya gabatar kan kisan jami'an tsaro
  • Ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar cewa miyagun da ke da hannu a kisan gillar sun fuskanci hukuncin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa a ranar Talata, 19 ga watan Maris, ta bada umurnin gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa sojoji 16 a jihar Delta.

Majalisar ta bada wannan umurnin ne ga kwamitocinta na sojoji, tsaro, sojojin sama da na ruwa, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Abin da majalisar dattawa ta buƙaci Tinubu ya yi wa iyalan sojojin da aka kashe a Delta

Majalisar dattawa ta fara bincike
Majalisar dattawa ta fara bincike kan kisan sojoji 16 a Delta Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Wani umurni majalisar ta bayar?

Majalisar dattawa ta buƙaci kwamitocin da su haɗa hannu da hukumomin soji da hukumomin gwamnatin tarayya waɗanda tuni suka fara bincike kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattawan ta kuma yi shiru na minti ɗaya don karrama jami’an da suka rasa ransu, tare da yin kira da a ɗauki ƙarin jami’an ƴan sanda da horas da su domin rage ayyukan ƴan sanda da sojoji ke yi.

Majalisar dai ta amince da hakan ne biyo bayan ƙudirin da Sanata Abdulaziz Yar’adua (APC, Katsina ta tsakiya) ya gabatar a zaman majalisar, rahoton da jaridar The Guardian ya tabbatar.

An yi wa ƙudurin taken "Kisan sojojin Najeriya a yankin Okuama, jihar Delta da kuma wajabcin gudanar da bincike cikin gaggawa."

Majalisar ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa an gano waɗanda ke da alhakin wannan aika-aika, tare da cafke su, gurfanar da su gaban kuliya don girbar abin da suka shuka ta hanyar bin doka da oda.

Kara karanta wannan

Shirin tsige mataimakin gwamnan PDP ya yi nisa bayan majalisa ta dauki sabon mataki

Oberevwori ya gana da Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oberevwori, ya gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa da ke Aso Rock Villa a birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya gana da shugaban ƙasan ne kan kisan da aka yi wa sojoji a ƙauyen Okuama na ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng