An Samu Bullar Cutar Zazzabin Lassa a Kananan Hukumomi 7 a Arewacin Najeriya

An Samu Bullar Cutar Zazzabin Lassa a Kananan Hukumomi 7 a Arewacin Najeriya

  • An samu bullar cutar zazzabin Lassa a kananan hukumomi bakwai na jihar Bauchi kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar
  • Gwamnatin jihar ta zayyana kananan hukumomin da abin ya shafa da suka hada da Bauchi, Toro, Kirfi, Tafawa Balewa, Dass, Ganjuwa da Alkaleri
  • Hukumar Yaki da Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce Bauchi, Ondo da Edo ke da kashi 75 na adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Lassa a kananan hukumomi bakwai na jihar.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Bauchi, Toro, Kirfi, Tafawa Balewa, Dass, Ganjuwa da Alkaleri.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ba hukumar Kwastam sabon umarni kan kayan abincin da ta kwace

An samu bullar zazzabin Lassa a jihar Bauchi
Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Lassa a jihar. Hoto: @NCDCgov
Asali: UGC

Yaduwar zazzabin Lassa a Najeriya

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa har yanzu dai babu wani bayani na kididdiga a hukumomin lafiya na Bauchi kan adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar a 2023/2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wani rahoto daga Hukumar Yaki da Cututtuka ta Kasa (NCDC) ya nuna cewa jihar Ondo, Bauchi, da Edo ne ke da kashi 75 cikin 100 na adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da zazzabin Lass a kasar nan.

Rahoton Premium Times ya nuna cewa an samu sabbin mutane 96 da suka kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 23 a jihohi 12 daga 19 zuwa 25 ga watan Fabrairu 2024.

Matakan kariya daga zazzabin Lassa

Tawagar ma’aikata daga ma’aikatun lafiya, gidaje da muhalli na jihar da kuma hukumar kare muhalli ta jihar Bauchi (BASEPA) sun fara aikin kula da masu cutar a yankunan da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane matsorata ne, sun cancanci hukuncin kisa, Remi Tinubu ta magantu a bidiyo

Jagoran tawagar, Mahmud Mohammed ya yi kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga kungiyar wayar da kan jama’a don kare kai daga kamuwa da cutar.

Mohammed ya gargadi 'yan jihar da su kasance masu rufe kayan abinci, guje wa shiga tarukan jama'a da kuma cudanya da masu cutar.

Hakimin Jama’a, Malam Isah Umar, ya yabawa gwamnatin jihar bisa kokarin da take yi na dakile wannan annoba.

Bakuwar cuta ta bulla jihar Kaduna

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa wata bakuwar cuta ta bulla a asibitin sojojoji na 44 da ke jihar Kaduna, wadda ta kashe ma'aikatan lafiya da wanda ke dauke da ita.

Birgediya Janar S.O Okoigi ya fitar da sanarwar bullar cutar a wata sanarwa da ya fitar a ranar 21 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel