Hukumar EFCC Ta Shiga Sabuwar Matsala Kan Tuhumar Tsohon Gwamna, Bayanai Sun Fito

Hukumar EFCC Ta Shiga Sabuwar Matsala Kan Tuhumar Tsohon Gwamna, Bayanai Sun Fito

  • An shigar da ƙorafi mai ƙarfi kan hukumar EFCC bisa tuhumar da take yi wa tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
  • Tun bayan da ya bar ofis bayan kammala wa'adinsa na shekara takwas, hukumar ta sa ido kan tsohon gwamnan
  • A halin da ake ciki, ƙungiyar Kogi In Diaspora Association (KIDA) ta caccaki hukumar EFCC bisa rashin adalcin da ta yi wa tsohon gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƴan Kogi mazauna ƙasashen waje (KIDA) ta ɗau mataki kan hukumar EFCC, tare da yin kira da a kawo ƙarshen abin da suke gani a matsayin cin mutuncin tsohon Gwamna Alhaji Yahaya Bello.

Jaridar Leadership ta ce a wata wasiƙa mai dauke da kwanan watan 9 ga watan Fabrairun 2024, zuwa ga ƙungiyoyi daban-daban na ƙasa da ƙasa, mai ba da shawara na ƙungiyar, Seyi Olorunsola, ya bayyana damuwarsu tare da neman a shiga tsakani.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun sace gomman mutane

An shigar da korafi kan hukumar EFCC
Hukumar EFCC ta taso Yahaya Bello a gaba tun bayan da ya bar mulkin jihar Kogi Hoto: Yahaya Bello, EFCC
Asali: Facebook

Wasiƙar, wacce aka rabawa manema labarai a Abuja a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu, ta yi kira ga ofisoshin diflomasiyya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da su gaggauta shiga tsakani ta hanyar amfani da tasirinsu, rahoton Blueprint ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me wasiƙar ƙungiyar KIDA ke cewa?

Wasiƙar ta yi magana kan zargin da hukumar EFCC ta yi wa tsohon Gwamna Bello a baya-bayan nan, na zargin almundahanar N80bn kafin ya hau mulki a shekarar 2015.

Wasiƙar tana cewa:

"Ƙungiyarmu ta damu matuƙa game da yadda ake ci gaba da fuskantar barazana ga ƴancin ƴan Nijeriya, musamman abin da hukumar EFCC ta yi a baya-bayan nan.
"Takamammen al’amarin da ke faruwa ya ƙunshi zargi marar tushe da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.
"Mun ga abin ban mamaki ne a ce mutumin da ba shi a kan mulki na iya yin almubazzaranci da irin wannan maƙudan kuɗade.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun kai hari a jihar Arewa, sun halaka mutane masu yawa

"Bugu da ƙari, da’awar da EFCC ta yi a shekarar 2021, na zargin gwamna Bello da karkatar da N20bn na kuɗaɗen Kogi a wani bankin kasuwanci, bankin ya musanta hakan, daga bisani an kori shari’ar.

Kira domin a ɗauki mataki

Ƙungiyar ta bayyana cewa yadda kafafen yaɗa labarai ke magana kan batun na ɓata sunan mutane irinsu Gwamna Bello da sanya damuwa kan yadda EFCC ke amfani da ikonta ba ta hanyar da ya dace ba.

Sun bayyana cewa yadda EFCC ke hantarar tsohon gwamnan ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, ya saɓawa ƙa'idojin gaskiya da adalci.

Sun yi kira ga ofisoshin diflomasiyya na ƙasa da ƙasa da cibiyoyi da su yi amfani da hanyoyin da ke da tasiri wajen magance wannan batu.

Sun ce cin zarafin da hukumar EFCC ke yi na barazana ga ƴanci da haƙƙin ƴan Najeriya.

Gwamnatin Kogi Na Bayan Yahaya Bello

Kara karanta wannan

AFCON 2023: Gwamnatin Tinubu ta yi wa Super Eagles muhimmin alkawari saboda kai wa wasan karshe

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kogi ta yi ƙorafi kan yadda wasu ƴan siyasa ke yunƙurin ɓata sunan tsohon gwamnan jihar Yahaya Bello.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Usman Ododo, ta ce wasu ƴan siyasa na amfani da hukumar EFCC domin ganin sun tozarta tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel