Barazanar Kisa: Gwamnan PDP a Arewa Ya Ba Remi Tinubu Hakuri, Ya Daukar Mata Alkawari

Barazanar Kisa: Gwamnan PDP a Arewa Ya Ba Remi Tinubu Hakuri, Ya Daukar Mata Alkawari

  • Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya yi Allah wadai da kalaman wani malamin addini kan matar shugaban kasa, Remi Tinubu
  • Gwamnan ya ba uwargidar shugaban kasa, Bola Tinubu hakuri kan abin takaici da ya faru inda ya ce hakan ba zai sake faruwa ba
  • Wannan na zuwa ne bayan wani malamin Musulunci ya bayyana cewa Remi Tinubu ta cancanci kisa a matsayinta na Kirista

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi martani kan barazanar kisa ga matar shugaban kasa, Remi Tinubu.

Bala ya ba Remi hakuri inda da ya yi alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba da cewa za su dauki mataki kan haka .

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba Ali Nuhu mukami a hukumar fina-finai saboda Rarara? Gaskiya ta bayyana

Gwamna PDP ya yi martani kan barazanar kisa da sani malamin Musulunci ya yi fa Remi Tinubu
Gwamna Bala ya yi Allah wadai da kalaman barazanar kisa da malamin ya yi ga Remi Tinubu. Hoto: Senator Bala Mohammed, Remi Tinubu.
Asali: Facebook

Martanin gwamnan Bauchi kan lamarin

Gwamnan ya yi Allah wadai da barazanar inda ya de wannan babban abin takaici ne a kasar Najeriya baki daya, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Ministan Abuja ya bayyana haka ne a fadar Mai Martaba, Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu.

Ya ce ya ji babu dadi kan wannan lamari inda ya ce uwar gidan shugaban ta nuna jarunta sosai duk da barazanar.

"A madadin Mai Martaba Sarkin Bauchi da al'ummar jihar nan muna baki hakuri kan wannan abin takaici, ba zai sake faruwa ba."

- Baa Mohammed

Asalin abin da ya faru game da barazanar

Wannan ba zuwa ne bayan wani malamin addinin Musulunci ya yi barazara ga rayuwar Remi Tinubu inda ya ce ta cancanci kisa.

Daga bisani, malamin ya fito ya ba da hakuri inda ya yi dana sanin furta wadannan kalamai da suka jawo cece-kuce, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Abdul Ningi: Gwamnan PDP a Arewa ya nuna goyon bayansa ga sanata, ya fadi matakin da zai dauka

'Yan Najeriya da dama sun bukaci a hukunta malamin duk da ba da hakuri da ya yi domin ya zama iznin ga saura.

Remi ta magantu kan barazanar

Kun ji cewa uwar gidan shugaban kasa, Remi Tinubu ta yi martani kan barazanar da wani malami ya yi mata.

Remi ta bayyana cewa a yanzu a wannan shekarun nata bai kamata ta ji tsoron mutuwa ba.

Hakan ta biyo bayan barazana da wani malami ya yi da cewa ta cancanci kisa saboda addininta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel