Dole a dinga tilasta maza suna auren mata biyu ko zinace-zinace zai ragu - In ji wata mawakiya
- Kwararriyar mawakiyar yabo ta addinin Kirista ta kasar Ghana, ta bayyana goyon bayanta na auren mace fiye da daya
- Ta ce, a maimakon namiji ya ajiye 'yam mata a waje, zai fi idan ya kara aure
- Mawakiyar ta bayyana yadda mata suke tara samari biyar zuwa shida a lokaci daya, saboda kawai daya baya iya kula dasu
Kwararriyar mawakiyar yabo ta addinin Kirista, Stella Seal wacce aka fi sani da Stella Dugan ta bayyana goyon bayanta ga maza na auren mace fiye da daya. Ta ce, hakan zai shawo kan yaduwar neman mata da mazan aure ke yi.
Mawakiyar addinin Kiristan ta kasar Ghanan ta jaddada cewa, barin a cigaba da wannan tsarin zai hana maza da mata lalata a al'umma.
Ta sanar da hakan ne a wata tattaunawa da Becks ta yi da ita a shirin Becky E, wanda har yanzu ba a fitar ba.
KU KARANTA: Tirkashi: Karuwa ta shiga kotu da katon maciji a lokacin da ake shirin yanke mata hukunci
A yayin tattaunawa da Becky, ta tabbatar da cewa in har mijinta ya bukaci kara aure, ba za ta damu ba. Kamar yadda ta ce, "Idan har namiji zai iya daukar dawainiyar mace fiye da daya, a maimakon ya tara 'yam mata a waje, ai zai fi idan ya kara auren.
"Idan kana son matarka da gaske, ka yi kokarin ganin ka daidaita aurenku. Na zanta da 'yam mata masu yawa. Akwai wadanda suka tabbatar min da cewa suna da samari biyar zuwa shida, saboda basu san wanda zai basu kulawar da suke bukata ba."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng