Tsoho Mai Shekara 85 Ya Shiga Hannu a Kano Bisa Zargin Garkuwa da ‘Dan Shekara 3

Tsoho Mai Shekara 85 Ya Shiga Hannu a Kano Bisa Zargin Garkuwa da ‘Dan Shekara 3

  • Rundunar NSCDC ta reshen jihar Kano tayi ram da wani tsoho da ake zargi da laifin yin garkuwa da mutum a Ungogo
  • Bayanan da kakakin dakarun ya yi wa duniya ya nuna za a tuhumi wannan ‘dan shekara 85 da laifin dauke karamin yaro
  • Ba a kai ga karbar kudi daga hannun iyayen yaron mai shekaru 3 ba asirin wannan mutumi – Ibrahim Usman ya tonu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Dakarun hukumar NSCDC na reshen Ungoggo a jihar Kano, sun cafke wani tsoho da ake zargi da hannu wajen yin laifuffuka.

Rahoton Daily Trust ya nuna ana zargin wannan tsoho da laifin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa daga hannun bayin Allah.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya maida zazzafan martani kan garkuwa da ɗalibai da ƴan gudun hijira a jihohi 2

Garkuwa da mutane
Ana zargin ‘dan shekara 85 da garkuwa da mutane a Kano Hoto: Nigeria Security and Civil Defence Corps
Asali: Facebook

Garkuwa da mutane a jihar Kano

An cafke Ibrahim Usman ne a rukunin gidajen ‘Yar’adua da ke unguwar Rimin Kebe a karamar hukumar Ungoggo da ke birnin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’in hulda da jama’a na NSCDC ya shaida cewa wanda ake zargi ya dauke wani karamin yaro mai shekara uku ne ya boye shi.

Ana zargin tsohon ya sace yaron ne daga hannun makwabta, sai ya yi yunkurin boye shi a gidan wani abokinsa da ke unguwar Hotoro.

Aboki ya tona asirin garkuwa da yaro

Punch ta ce abokin ya ji kanshin rashin gaskiya a lamarin, ya ki yarda ya boye yaron a hannunsa, a madadin haka ya sanar da jama’a.

A haka ne ‘yanuwa da abokan arziki a unguwar Rimin Kebe wadanda suke ta faman cigiyar yaron suka samu labarin halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da fursuna ya karbe bindigar jami'i, ya harbe wani mutum

Ba wannan ne karon farko da aka ji irin wannan mummunan labarin satar yara a Kano ba, a baya za a iya tuna labarin wata Hanifah.

Ganin haka sai mutumin da ake tuhuma da laifi ya tsere, daga baya jami’an NSCDC na reshen karamar hukumar Ungoggo suka cafke shi.

Za a yi shari'ar garkuwa da mutane

Daily Post ta rahoto jami’in huldan yana cewa tsohon ya karbi lamba daga yaron da ake zargin ya dauke, amma bai taba kiran wayar ba.

Yanzu bincike ya yi nisa, NSCDC ta ce da zarar an kammala, za ta shigar da kara kotu inda Remi Tinubu ta ke so a rika kashe mai laifi.

Laifin satar danyen mai a N/Delta

A Neja-Delta kuma, kwanaki aka ji labari sojojin kasa sun ci karo da wani gari a jihar Ribas da ake satar danyen mai hankali kwance.

Kara karanta wannan

Daliban jami'a 4 sun lakadawa abokin karatunsu duka har ya mutu, ‘yan sanda sun dauki mataki

N40, 000 rak ake biya a haka rami a kauyen Rumuekpe, daga nan sai tsageru su shiga hako danyen mai, su saida a kasuwar duniya.

Wani babban jami’in soja ya ce a maimakon a fasa bututun danyen mai, an samu cigaba a yanzu domin man ake hakowa kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng