Hukumar NSCDC Ta Cafke Masu Kwacen Wayoyi 5 a Kano, Ta Farautar Masu Siyan Wayoyin

Hukumar NSCDC Ta Cafke Masu Kwacen Wayoyi 5 a Kano, Ta Farautar Masu Siyan Wayoyin

  • Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Kano ta kama wadansu mutane biyar da ake zargin masu kwacen wayoyi ne
  • Hukumar ta tabbatar da cewa yanzu haka sun bazama neman sauran mutane biyu wadanda suke siyan wayoyin sata
  • Hukumar, ta bakin daraktan hulda da jama’a, Ibrahim Abdullahi ta ce an kama yaran ne a ranar Talata 23 ga watan Mayu

Jihar Kano - Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Kano ta samu nasarar kama wadansu mutane biyar ake zargi da kwacen wayoyi a Kano.

Hukumar a yanzu haka tana neman wadansu mutane biyu da ake zargin suna siyan wayoyin sata.

Hukumar NSCDC
NSCDC Ta Cafke Masu Kwacen Wayoyi 5 a Kano. Hoto: Daily Post
Asali: UGC

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bakin daraktan hulda da jama’a ta hukumar, Ibrahim Abdullahi ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a ranar Talata 23 ga watan Mayu a Sabon Gari da ke karamar hukumar Fagge a jihar.

Kara karanta wannan

Kwacen Waya: Fusatattun Matasa Sun Sake Kone Adaidaita Sahu Ta Barayin Waya a Kano

Hukumar ta bayyana sunayen wadanda aka kaman

Sanarwar kamar yadda rahotanni suka tattaro ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wadanda ake zargin Faisal Usman mai shekaru 28 da Mansur Isa mai shekaru 38 sai kuma Abdullahi Bashir, 25 da Ahmed Ibrahim, 21 sai kuma Zulkifil Bello mai shekaru 25.
“Suna aikata muggan laifuka a yankin Sabon Gari a karamar hukumar Fagge da ke jihar inda suke kwace wayoyin mutane da basu ji ba kuma basu gani ba.
“Jami’an mu na bangaren tattaro bayanin sirri yanzu haka sun bazama neman sauran wandanda suka hada kai, Abdullahi da Sunday wadanda sune suke siyan wayoyin sata da kuma layukan waya."

Hukumar ta tabbatar wa jama'a cewa za ta kawo karshen wannan matsalar

Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da yakin da duk wasu laifuka da suka sabawa doka a jihar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An Kama Masu Garkuwa Da Yan Kungiyar Asiri 26 A Fitaciyyar Jihar Arewa

A cewar hukumar:

“Hukumar mu rashen jihar Kano tana mai tabbatarwa jama’a cewa za ta ci gaba da yaki da masu kwacen waya a jihar dama sauran laifuka daban-daban da ke faruwa da suka sabawa doka, sannan za mu tabbatar da ba da kariya ga kadarorin gwamnati."

A kwanan nan ana yawan samun kwace-kwacen wayoyi da ake yi wa mutane musamman a cikin birnin Kano da abin ya yi kamari.

Fusatattun Matasa Sun Sake Kone Adaidaita Sahu Ta Barayin Waya a Kano

A wani labarin, mutane sun fusata a Kano yayin da suka kone adaidaita sahu bisa zargin ta masu kwacen waya ne.

Lamarin wanda ya faru a ranar Laraba 24 ga watan Mayu a birnin Kano ba shine karon farko ba mutane ke daukar doka a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel