Malamai Da Ɗalibai sun ranta a na kare bayan jin harbin bindigogin IPOB a makarantarsu a Imo

Malamai Da Ɗalibai sun ranta a na kare bayan jin harbin bindigogin IPOB a makarantarsu a Imo

  • Bayan jin harbe-harben wasu da ake zargin ‘yan IPOB ne a ranar Litinin har cikin makarantar sakandaren Comprehensive, dalibai sun ranta a na kare
  • Kamar yadda bayanai suka kammala, al’amuran makarantar wacce take karamar hukumar Njaba da ke jihar Imo sun rikice bayan jin harbin
  • Dama daliban su na tsaka da rubuta jarabawa ne ‘yan bindigan suka afka musu su na ta harbe-harbe a iska su na banka wa baburan malamai da dalibai wuta

Jihar Imo - Harbe-harben IPOB ya yi sanadiyyar fatattakar dalibai a wata makarantar sakandare ta Comprehensive da ke karamar hukumar Njaba a jihar Imo a ranar Litinin.

‘Yan bindigan da ake zargin ‘yan IPOB ne sun afka wa makarantar inda suka dakatar da dalibai daga rubuta jarabawar su.

Malamai Da Ɗalibai sun ranta a na kare bayan jin harbi bindigogin IPOB a makarantarsu a Imo
Mambobin kungiyar IPOB. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Daliban Zamfara 75 da aka sace sun samu 'yanci bayan kwanaki 11

Bisa ruwayar Daily Trust, daliban su na shirin rubuta jarabawar darasin Turanci ne na JSSCE kwatsam ‘yan bindigan suka hargitsa su.

Daga daliban har malamai ba su yi kasa a guiwa ba suka tsere bayan jin harbe-harbe a iska.

‘Yan bindigan sun banka wa ababen hawan malamai da dalibai wuta

‘Yan bindigan sun ci gaba da banka wa baburan malamai da daliban makarantar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Duk da dai ba a samu labarai akan mutane nawa suka halaka ba har yanzu, amma an samu wani bidiyo wanda aka hango dalibai da malamai suna gudu sakamakon harbe-harben don tseratar da rayukan su.

Daily Trust ba ta samu damar tattaunawa da jami’in hulda da jama’ar ‘yan sandan yankin ba, CSP Mike Abattam, don jin ta bakin sa.

Duk ranar da Kanu zai bayyana gaban kotu, wajibi ne mazauna Imo su zauna a gida bisa umarnin IPOB

Kara karanta wannan

Mata a Afghanistan sun yi dandazo don nuna goyon bayansu ga mulkin Taliban

Dama IPOB ta umarci kowa ya zauna a gida ranar Litinin din neman a saki shugaban su, Nnamdi Kanu, waqnda yanzu haka yake fuskantar hukunci a babbar kotun Abuja.

Ana tunanin ci gaba da zama a gidan har ranar Talata domin ranar ake tunin Kanu zai bayyana gaban kotu.

Baya ga ranar Litinin, kungiyar ta umarci kowa da ya zauna a gida a duk wata rana da Kanu zai bayyana a gaban kotu.

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

A wani kabarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Kara karanta wannan

An kama fasto da ta mayar da coci gidan da ake ɗirka wa mata ciki suna haihuwar jarirai ana sayarwa attajirai

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel