An Gudu Ba a Tsira Ba: Jami’an Tsaro Sun Cafke Fursunan da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Katsina

An Gudu Ba a Tsira Ba: Jami’an Tsaro Sun Cafke Fursunan da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Katsina

  • Fursuna na karshe da hukumar kula da gidajen yarin jihar Katsina ta baza komar kama shi ya shiga hannu a Kaduna
  • A cikin watan Oktoba ne fursunoni biyu da ke jiran hukuncin kotu suka samu nasarar tserewa daga gidan yarin inda suka fantsama gari
  • Sai dai hadin guiwar hukumomin jami'an tsaro ya taimaka wajen kama Abba Kala, daga bisani kuma aka kama Musa Isah a Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

JIhar Katsina - Hukumar kula da gidajen yarin Najeriya (NcoS), jihar Katsina ta ce jami'an tsaro sun kamo dayan fursonan da ya tsere daga gidan yarinta a watan Oktoba.

Wata sanarwa daga ASC Najibullah Idris, kakin hukumar da ya fitar ranar Laraba ya ce an kama fursunan ne a ranar Talata a garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Inna lillahi: Mayakan Boko Haram sun kai sabon farmaki garin Chibok, sun yi ta'adi

An kama fursunan da ya tsere daga gidan yarin Katsina
Jami'an tsaro sun kamo fursonan da ya tsere daga gidan yarin Katsina a watan Oktoba. Hoto: @Najibkunduru
Asali: Twitter

Abin da hukumar gidajen yari ke cewa kan kama fursunonin biyu

Inda za a iya tunawa fursunoni biyu da ke tsare a gidan yarin Katsina sun tsere a ranar 17 ga watan Oktoba yayin da su ke jiran a yanke musu hukunci, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Guardian ta ruwaito cewa jami'an tsaro sun samu nasarar kama Ibrahim Muhammad Lawal, da aka fi sani sani da Abba Kala, daga bisani kuma jami'an tsaron suka kama Musa Isah.

Ya ce:

"Zuwa yanzu muna sanar da al'umma cewa dukkan fursunonin biyu sun zo hannu, don haka kowa ya yi rayuwarsa ba tare da fargaba ba.
"Shugaban hukumar gidajen yari na kasa Haliru Nababa ta bakin shugaban hukumar na Katsina, Muhammad Abdulmumin Haruna, na jinjinawa jami'an tsaron da suka kamo fursunonin."

Saurayi ya kashe budurwarsa sa saboda ta nemi ya ba ta N5,000

Kara karanta wannan

Harin sojojin Najeriya kan farar hula: Miyetti Allah ta kafa wa Tinubu wani muhimmin sharadi

A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta ce wani dan shekara 19 Muhammad Ibrahim a jihar Bauchi ya kashe budurwarsa Emmanuella Ande kan naira dubu biyar.

A ranar Laraba ne 'yan sanda suka kama matashin, bayan da ya caka wa budurwar wuka a kahon zuci a wani dakin da ta kama a 'Bayan Gari', inda mutane su ka jiyo ihunta suka kai dauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel