An nada Farfesa Sagir sabon shugaban jami'ar Bayero

An nada Farfesa Sagir sabon shugaban jami'ar Bayero

– Jami’ar Bayero ta Kano ta nada sabon Shugaba

– Farfesa Sagir Abbas ne sabon Shugaban Jami’ar

– Shugaban Majalisar Gudanarwa na jami'ar, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya tabbatar da nadin

A jiya Asabar aka tabbatar da nadin Farfesa Sagiru Abbas, a matsayin sabon Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano watau BUK.

Wannan ya biyo bayan hukuncin shaidar tabbaci da Majalisar Gudanarwa da Jami’ar ta dauka.

Hakan na kunshe ne cikin wasikar tabbatar da nadi mai dauke da sa hannun shugaban Majalisar, Farfesa Ibrahim Gambari, wadda da aka gabatar wa sabon shugaban jami'ar a ranar Asabar.

A cikin wasikar, Farfesa Gambari ya sanar cewa Mista Abbas zai kasance shugaban jami'ar har na tsawon wa'din shekaru biyar wanda zai fara aiki daga ranar 18 ga watan Agusta.

Farfesa Sagir dai Malamin Jami’ar ne tun asalin sa, kuma babban Farfesa ne a Sashe da Tsangayar Koyon Karantarwa na Makarantar wanda kuma ya rike wasu mukaman a baya.

Farfesa Sagir Aminu Abbas ya doke sauran abokan takaransa a zaben al'ummar jami'a, wani babban mataki na zaben Shugaban Jami'ar Bayero da aka gudanar a ranar Laraba.

Farfesa Abbas wanda tsohon mataimakin shugaban jami'ar ne ya samu kuri'u 1,026, inda ya doke wanda ke biye da shi, Farfesa Adamu Idris Tanko, mai kuri'u 416.

KARANTA KUMA: Rayuka 10 sun salwanta yayin da 'yan sanda suka fafata da 'yan daban daji a Katsina

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, sauran 'yan takarar da suka nemi kujerar shugabancin Jami'ar sun hadar da Muhammad Dikko wanda ya samu kuri'u 10 da kuma Dalhatu Balarabe, wanda ya samu kuri'u biyar kacal.

A jawaban da gabatar, sabon Shugaban Jami'ar ya yi kira ga al’ummar jami’ar da su ba shi dukkanin goyon bayan da yake bukata don daukaka cibiyar ilimin zuwa babban matsayi.

Yayin da yake ba da tabbacin yin duk mai yiwuwa wajen ciyar da jami’ar gaba, Farfesa Abbas yayi alkawarin cewa wannan tafi ya ta 'mu duka' kuma za ta hadar da kowa da kowa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel