Shugaban Miyetti Allah Ya Shiga Hannun Jami’an Tsaro, an Bayyana Matakin Gaba

Shugaban Miyetti Allah Ya Shiga Hannun Jami’an Tsaro, an Bayyana Matakin Gaba

  • Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN a jihar Adamawa, Alhaji Jaoji Isa ya shiga hannun rundunar ‘yan sanda kan wasu zarge-zarge
  • Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ita ta tabbatar da haka inda ta ce ana zarginsa da tatsar kudaden fiye da miliyan 2
  • Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa – Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta cafke shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar, Alhaji Jaoji Isa.

Rundunar ta kama shugaban MACBAN din ne kan zargin badakalar makudan kudi har naira miliyan 2.4.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya yi muhimman nade-nade a kananan hukumomin jiharsa

'Yan sanda sun cafke shugaban Miyetti Allah kan wasu zarge-zarge
Rundunar ta kama Jaoji ne kan tatsar kudade a hannun jama'a. Hoto: Nigerian Police Force, Jaoji Isa.
Asali: UGC

Menene ake zargin Jaoji da aikatawa?

Ana zargin shugaban kungiyar da karbar kudade a hannun jama’a ba bisa ka’ida wanda ya sabawa doka, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje ya fitar ga manema labarai.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, CP Dankombo Morris ya umarci gudanar da bincike domin tabbatar da dakile karbar kudi a hannun jama’a.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa duk wadanda aka samu da badakalar za su fuskanci fushin hukuma, cewar New Telegraph.

Ya kara da cewa irin wannan hali ya na kara dakile kokarin hukumar wurin tabbatar da kawo karshen almundahana.

Bukatar Miyetti Allah kan Igboho

Har ila yau, Kungiyar Miyetti Allah ta bukaci gwamnatin tarayya ta kama dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke shugaban ƴan bindiga da tawagarsa ta addabi jihar Katsina

Kungiyar na zargin Igboho da neman korar Fulani daga yankinsa inda ya yi barazana gare su a cikin wani faifan bidiyo.

Shugaban kungiyar ta kasa, Baba Othman shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu.

Sojoji sun ya magana kan Igboho

Kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun yi martani kan kalaman mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo Igboho.

Rundunar ta ce idan har kalamansa za su inganta zaman lafiya babu damuwa amma sabanin haka kuma ya wuce gona da iri.

Wannan na zuwa ne yayin da Igboho ya fito a cikin wani faifan bidiyo da ya ke barazana ga Fulani Makiyaya a yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel