Covid-19: FOA ta fidda kasashe 27 da za su fuskanci matsalar karancin abinci
- Annobar korona ta fara angiza wasu kasashen duniya cikin matsalar karancin abinci kamar yadda hukumomin kula da aikin noma da samar da abinci na majalisar dinkin duniya FAO da WFP suka nuna
- Najeriya, Kamaru, Liberia, Mali da kuma Nijar, suna cikin jerin kasashen da ta fitar a rahoton
- Binciken ya yi gargadin cewa, a watanni masu zuwa, annobar korona za ta yi mummunan tasirin jefa wasu al'ummomin cikin matsananciyar yunwa da karancin abinci
A yayinda duniya ke ci gaba da fama da annobar korona, wani sabon nazari da Hukumomin Kula da aikin noma da samar da abinci na Majalisar Dinkin suka gudanar, ya nuna cewa kasashe 27 za su fuskanci babbar matsala.
Binciken Hukumomin Kula da aikin noma da samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya FOA da WFP, ya nuna cewa, nan da watanni kadan, za'a samu karin yawan mutane da matsananciyar yunwa za ta addaba.
Hukumomin sun yi gargadin cewa, akwai akalla kasashen duniya 27 da za su iya fuskantar fari da zai janyo karancin abinci da kuma matsananciyar yunwa sakamakon mummunan tasirin da annobar korona take haifar wa.
Bincike ya ambaci cewa, muddin likafar annobar korona ta ci gaba babu sassauci, wasu kasashe musamman a nahiyar Afrika da Asia, za su fuskanci barazana ta karancin abinci.
Wasu daga cikin kasashen da aka fidda kiyasi a kansu sun hadar da:
1. Afghanistan
2. Bangladesh
3. Haiti
4. Venezuela
5. Iraq
6. Lebanon
7. Sudan
8. Syria
9. Burkina Faso
10. Kamaru
11. Liberia
12. Mali
13. Nijar
14. Najeriya
15. Mozambique
16. Sierra Leone
17. Zimbabwe
KARANTA KUMA: Rundunar 'yan sanda ta kori jami'anta hudu saboda laifin cin amanar kasa
Da yake magana dangane da rahoton, darekta janar na hukumar FOA, Qu Dongyu, ya ce wannan shi ne mafi munin fari da karancin abinci da kasashen za su fuskanta a wannan zamani.
Mista Dongyu ya ce kuma doriyar wata musiba ce a kan kasashen baya da fama da matsananciyar yunwa da ake yi a cikinsu tun kafin bullar annobar korona.
A cewarsa, tasirin annobar ya kara ta'azzara matsalolin da ke haddasa yunwa da ake fama da su ciki har da; matsin tattalin arziki, rashin tsaro, sauye-sauye da dumamar yanayi, cututtukan dabbobi da kuma na tsirrai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng