'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Kan Sojoji, Sun Kashe Soja Tare da Bayin Allah da Yawa

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Kan Sojoji, Sun Kashe Soja Tare da Bayin Allah da Yawa

  • Ƴan bindiga sun kai hari kan sojojin Najeriya, sun kashe soja ɗaya tare da mutane da yawa a kananan hukumomi 2 a jihar Benuwai
  • Kwamandan rundunar OPWS, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia, ya tabbatar da kashe sojan, amma ya ce dakarun sun halaka yan bindiga uku
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Benuwai, Catherine Anene, ta ce tana da labarin wasu mutane sun shiga jejin Kwande amma babu kisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Wasu miyagu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun halaka mutane da yawa ciki harda jami'in soja a hare-haren da suka kai a jihar Benuwai

Kamar yadda jaridar The Nation ta tattaro, maharan sun tafka wannan ta'addanci ne a kauyukan ƙananan hukumomin Kwande da Apa ranar Asabar da Lahadi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe babban jigon jam'iyyar PDP da wasu mutum 2 a Arewacin Najeriya

Dakarun sojin Najeriya.
Yan Bindiga Sun Kashe Sojan Najeriya Tare da Bayin Allah Masu Yawa a Benue Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun farmaki kauyen Maav-Ya a yankin Kwande da kauyukan Turan Jato-Aka da Ochumekwu a yankin Apa duk a jihar Benuwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindigan suka kai hare-haren

Rahoto Daily Post ya nuna cewa mutane da dama sun rasa rayuwarsu yayin da wasu da yawa suka ɓata sa'ilin da ƴan bindiga suka farmaki kauyen Udedeku a ƙaramar hukumar Kwande.

Kwamandan rundunar sojin Operations Whirl Stroke, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia, ya tabbatar da kashe jami'in soja ɗaya yayin hira da ƴan jarida a Makurɗi ranar Litinin.

Ya ce:

"Wasu ‘yan bindiga sun farmaki sojojin da aka tura kauyen Ochumekwu da ke karamar hukumar Apa, inda suka kashe jami'i daya tare da raunata guda daya.
“A martanin da suka mayar, Sojojin sun kashe uku daga cikin ƴan bindigan tare da jikkata wasu da dama. Sun kwato AK47 guda daya da alburusai daga hannun maharan."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu galaba, sun halaka ƴan bindiga da yawa a jihohi 3 na Arewa

Sai dai kwamandan rundunar bai iya tabbatar da harin Kwande ba amma ya ce yanzu haka sojoji sun fara aikin tsaftace ƙaramar hukumar daga ƴan bindiga da suka kwarara.

Da aka tuntuɓe ta kan lamarin, mai magana da yawun ƴan sandan Benuwai, Catherine Anene, ta ce ta samu labarin wasu sun kutsa cikin dajin Kwande amma ba a kashe kowa ba.

"Labarin da na samu shi ne wasu mutane sun shiga daji a Kwande amma ban ji batun kisan rayuka ba," in ji ta.

Masu akidar Boko Haram kaɗan suka rage a Borno

A wani rahoton kuma Gwamnatin Borno ƙarƙashin Farfesa Babagana Zulum, ta ce kashi 95 cikin 100 na masu tsattsaurar akidar Boko Haram sun mutu ko sun tuba.

Mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro, Ishaq Abdullahi, ya faɗi yadda mafi yawan waɗanda suka kafa kungiyar suka mutu

Asali: Legit.ng

Online view pixel