'Yan Sanda Sun Cafke Masu Kera Makamai Ga 'Yan Bindiga a Jihar Arewa

'Yan Sanda Sun Cafke Masu Kera Makamai Ga 'Yan Bindiga a Jihar Arewa

  • Dubun masu ƙera makamai a jihar Benue ta cika bayan jami'an rundunar ƴan sandan jihar sun yi caraf da su a jihar
  • Waɗanda ake zargin dai sun shiga hannu nr bayan an samu bayanan sirri kan ayyukan da suke gudanarwa na ɓarna
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da cafke waɗanda ake zargin inda ya ce za a miƙa su kotu nan bada jimawa ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta kama wasu masu ƙera bindigu mutum uku a yankin Agu da ke ƙaramar hukumar Vandekiya ta jihar.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Emmanuel Adesina ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar ƴan sandan jihar da ke Makurdi, babban birnin jihar, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun dira kan ƴan bindiga, sun kashe su da yawa sun ceto mutum 40 a Arewa

Yan sanda sun cafke masu kera makamai
Masu kera makamai sun shiga hannun 'yan sanda a Benue Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa an samu nasarar cafke mutanen ne bayan an samu bayanan sirri kan ayyukansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Bayan bayanan da aka tattara game da cinikin makamai a Agu, ƙaramar hukumar Vandeikya, an tura jami'an ƴan sanda don tattara bayanan sirri tare da kama waɗanda ake zargin.
"A ranar 7 ga watan Fabrairun 2024 da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, an kama wani Precious Ebuka Chukwu ɗan asalin Onitsha a jihar Anambra a Agu da ke karamar hukumar Vandeikya.
"A wajen binciken da aka yi kan wanda ake zargin, an ƙwato ƙananan bindigogi guda uku ƙirar cikin gida.

Yadda aka cafke masu ƙera makaman

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya jagoranci tawagar jami'an ƴan sandan zuwa maɓoyar masu kawo masa bindigun, rahoton Blueprint ya tabbatar.

Ƴa ce mutanen biyu masu suna Tyav Wuese da Tyav Terkuma, maƙera ne dake a garin Adikpo, a ƙaramar hukumar Kwande waɗanda suka kware wajen ƙera bindigogi.

Kara karanta wannan

Yan sanda da sojoji sun yi kazamin artabu da ƴan bindiga, sun samu nasara a jihar Arewa

Kwamishinan ƴan sandan ya kuma ƙara da cewa mutanen biyu masu ƙera bidingogin an yi caraf da su, inda za a miƙa su gaban kotu nan bada jimawa ba.

Ƴan Sanda Sun Cafke Riƙaƙƙen Mai Garkuwa da Mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, sun samu nasarar cafke wani riƙaƙƙen mai garkuwa da mutane.

Wanda ake zargin dai yana daga cikin mutane biyu da ake nema ruwa a jallo kan aikata laifukan sace-sacen mutane domin samun kuɗaɗen fansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel