'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Jigon Jam'iyyar PDP da Wasu Mutum 2 a Arewacin Najeriya

'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Jigon Jam'iyyar PDP da Wasu Mutum 2 a Arewacin Najeriya

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi ajalin babban jigon PDP, Alhaji Shafiu Abubakar, a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tare motoci a kan titin zuwa garin Maradun, suka buɗe wa fasinjoji wuta
  • Mazauna yankin sun yi kira da a ɗauki matakin kawon ƙarshen ƴan bindiga a yankin duba da nan ne mahaifar ƙaramin ministan tsaro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Tsagerun ƴan bindiga sun kashe babban jigon Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara, Alhaji Shafiu Abubakar, tare da wasu mutum biyu.

Maharan sun tafka wannan mummunar ɓarna ne a Danbaza junction da ke cikin yankin Maradun, hedkwatar ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun Kai mummunan farmaki kan Sojoji, sun kashe soja tare da bayin Allah da yawa

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Yan Bindiga Sun Kashe Babban Jigon PDP da Wasu Mutum Biyu a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Leadership ta tattaro cewa ‘yan bindiga sun matsawa matafiya a kan titin mai tsawon kilomita 10, wanda zai kai ka zuwa garin Maradun, suna kashe rayuka da sace wasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴadda ƴan bindiga suka kashe jigon PDP

A sabon harin na baya-bayan nan, ‘yan bindigar sun toshe titin da manyan duwatsu domin tare masu ababen hawan da ke hanyar zuwa garin Maradun.

Bayan tare motocin, ƴan bindigar sun buɗe wa fasinjoji wuta, inda suka kashe jigon PDP da wasu mutane 2 da ba a gano sunayensu ba, sun kuma jikkata wasu fasinjoji uku.

Rahoto ya nuna cewa an kashe Abubakar ne yayin da yake da burin tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukumar Maradun a zaɓen kananan hukumomin Zamfara mai zuwa.

Dama dai al'umma sun nuna damuwa kan ƙaruwar hare-haren ta'addancin ƴan bindiga a kan titin duk da cewa akwai jami'an sojoji da ƴan sanda a yankin.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata, sun bazama kan babban titi suna ƙone-ƙone kan hare-haren yan bindiga

Wane mataki ya kamata a ɗauka?

Mazauna yankin sun yi kira da a dauki tsattsauran mataki kan ‘yan bindigar da ke yankin ganin cewa Maradun ce mahaifar karamin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle.

Ko a ƴan kwanakin nan, Matawalle ya bukaci dakarun sojoji suka kara zage dantse a yakin da suke da ƴan bindiga musamman a jihohi uku, ciki harda Zamfara.

An kashe soja da wasu mutane a Benuwai

A wani rahoton mun kawo maku cewa Ƴan bindiga sun kai hari kan sojojin Najeriya, sun kashe soja ɗaya tare da mutane da yawa a kananan hukumomi 2 a jihar Benuwai.

Kwamandan rundunar OPWS, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia, ya tabbatar da kashe sojan, amma ya ce dakarun sun halaka yan bindiga uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel