Gwamnan Arewa Ya Roƙi Shugaba Tinubu Ya Taimaka Masa a Kokarin Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga

Gwamnan Arewa Ya Roƙi Shugaba Tinubu Ya Taimaka Masa a Kokarin Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga

  • Malam Dikko Radda ya buƙaci gwamnatin tarayya ta taimaka masa a kokarin da yake na kawo karshen ƴan bindiga a jihar Katsina
  • Gwamna Radda ya kuma jajantawa iyalan waɗanda hare-haren ƴan bindiga ya shafa yayin da ya ziyarci fusatattun matasan Wurma da suka yi zanga-zanga
  • Ya ce gwamnatinsa za ta turo jami'an tsaro 100 kauyen kuma ita za ta riƙa ba su abinci domin su yi aikin da ake bukata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Umaru Dikko Radda, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tallafa wa kokarin da jihar take yi wajen yaki da ‘yan bindiga.

Gwamnan ya yi wannan roko ne a lokacin da yake jawabi ga matasan ƙauyen Wurma da suka yi zanga-zangar adawa da munanan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa yankin.

Kara karanta wannan

Dattawa sun tsoma baki kan batun sojoji su kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu kan abu 2

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda.
Gwamna Radda Ya Roki Taimakin Gwamnatin Tinuɓu Domin Kawo Karshen Yan Bindiga a Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda Ph.D
Asali: Facebook

Yayin wannan ziyara da ya kai domin rarrashin masu zanga-zangar, Gwamna Raɗɗa ya jajantawa iyalan waɗanda hare-haren ya shafa, Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnatinsa zata yi aiki tare da jami’an tsaro domin zakulo maharan duk inda suka shiga tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Wane mataki Radda ya ɗauka kan ƴan bindiga?

Dikko Radda ya gaya wa masu zanga-zangar cewa gwamnatinsa za ta turo jami'an tsaro 100 zuwa ƙauyen Wurma kuma ita za ta riƙa ciyar da su kullum.

Ya bukaci su zabi mutum 10 da za su gana da shi a Katsina domin tsara hanyoyin da za su magance kalubalen da suke fuskanta, musamman ganin yadda watan Ramadan ke karatowa.

A kalamansa, Radda ya ce:

"Kuna da gaskiya ku yi zanga-zanga amma don Allah ku kwantar da hankalinku domin gwamnati na yin duk mai yiwuwa don dakatar da lamarin.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata, sun bazama kan babban titi suna ƙone-ƙone kan hare-haren yan bindiga

"Kalmomi ba za su iya bayyana alhinin da nake ji ba ga iyalan da suka rasa ’yan uwa a cikin wannan matsala ta rashin tsaro.
"Zuciyata tana tausayin kananan yaran da suka rasa iyayensu da kuma al’ummar da lamarin ya shafa. Ina tare da ku a cikin wannan lokaci mai zafi da wahala mara misaltuwa"

"Ina kira da a zauna lafiya kuma mu haɗa kai a wannan yanki," in ji Malam Dikko Raɗda.

The Nation ta tattaro cewa fustattun matasan kauyen Wurma sun yi zanga-zanga inda suka toshe titin Katsina-Dutsinma, suka hana matafiya wucewa.

Wani mazaunin Dutsinma da ya halarci wurin, Muniru Aminu, ya faɗa wa Legit Hausa cewa ba abinda zasu bi Dikko da shi sai addu'a da fatan alheri.

"Dikko har kuka ya yi, ni dai ban taɓa jin ina kaunar shugaba irin gwamnan mu ba, ya nuna damuwa ba kaɗan ba kuma matakan da ya ce zai ɗauka in sha Allahu za su kawo karshen lamarin.

Kara karanta wannan

"Ba zaku iya faɗa da ni ba" Shugaba Tinubu ya ɗau zafi, ya aike da saƙo mai ɗumi ga NLC

"Ya yi alƙawarin turo jami'an tsaro kuma zai zauna da wasu wakilan domin gano tushen matsalar, maganganun da ya yi da kaji kasan da gaske yake, Allah dai ya taimake shi."

Meyasa matasan suka fito zanga-zanga?

Tun farko mun kawo muku rahoton cewa fusatattun mazauna kauyen Wurma a karamar hukumar Kurfi sun tsohe babban titin Katsina-Dutsinma kan hare-haren ƴan bindiga.

Masu zanga-zangar sun hana matafiya wucewa, lamarin da ya tilasta wa ababen hawa canza hanya domin tafiya garuruwan da suka nufa a sassan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel