“Alkawaran Iska”: NLC Ta Mayar da Martani Mai Zafi Ga Tinubu, Ta Fada Masa Abu 1 da Zai Yi

“Alkawaran Iska”: NLC Ta Mayar da Martani Mai Zafi Ga Tinubu, Ta Fada Masa Abu 1 da Zai Yi

  • Shugaban kasa Bola Tinubu da shugaban NLC sun yi cacar baki sakamakon halin da ake ciki na matsin rayuwa a Najeriya
  • Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bukaci Tinubu da ya mayar da hankali wajen magance manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta
  • Hakan na zuwa ne bayan Tinubu, ya caccaki kungiyar kan zanga-zanga da ta yi a yankunan kasar, sannan ya gargadi NLC kan ci gaba da caccakar gwamnatinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

FCT, Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta caccaki Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan furucin da ya yi game da zanga-zangar gama gari da aka yi a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu.

Ku tuna cewa yayin da yake kaddamar da aikin layin dogo a Legas a ranar Alhamis, Tinubu ya ce kungiyar NLC ba ita kadai ce muryar 'yan Najeriya ba, sannan cewa ta fito ta yi takara a zaben 2027 idan har tana son shiga tsarin zabe ne.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya tsaida ranar fara rabon abinci tan dubu 42 da jihar da za a fara

An yi cacar baki tsakanin Tinubu da 'yan kwadago
“Alkawaran Karya”: Shugaban NLC Ya Yiwa Tinubu Wankin Babban Bargo, Ya Fada Masa Abu 1 da Zai Yi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

A ranar Juma'a, 1 ga watan Maris, kungiyar NLC ta bukaci shugaba Tinubu da ya mayar da hankali wajen magance tarin kalubalen da 'yan Najeriya ke fuskanta, maimakon cacar baki da 'yan kwadagon, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ka magance matsalolin Najeriya, NLC ga Tinubu

Da take martani a ranar Juma'a, a wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban NLC, Joe Ajaero, kungiyar ta bukaci Tinubu da ya nuna shaidar cika yarjejeniyar da suka cimma da 'yan kwadago cikin watanni tara da kafa gwamnatinsa.

Sai dai kungiyar ta shawarce shi da ya mayar da hankali wajen cika alkawuran da ya yi wa ‘yan Najeriya maimakon barazana ga kungiyoyin kwadago.

Sai kuma kungiyar kwadagon ta shaida wa shugaban kasar cewa ma’aikata ba sa neman aikinsa, don haka ya mayar da hankali wajen cika alkawuran da ya daukar wa ‘yan Najeriya maimakon yi masu barazana, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

"Ba zaku iya faɗa da ni ba" Shugaba Tinubu ya ɗau zafi, ya aike da saƙo mai ɗumi ga NLC

NLC ta fadi gaskiya game da tsaida zanga-zanga

A wani labarin, mun ji a baya c ewa kungiyar kwadago ta kasa watau NLC, tayi karin haske a game da dalilin dakatar da zanga-zangar lumanar da ta shirya.

Joe Ajaero wanda shi ne shugaban kungiyar NLC ta kasa ya bayyanawa manema labarai wannan, Tribune ta fitar da labarin a jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng