“Allah Ya Sa Malam Ya Hakura”: Jigon APC Ya Magantu Kan Sabanin Daurawa da Gwamnatin Kano

“Allah Ya Sa Malam Ya Hakura”: Jigon APC Ya Magantu Kan Sabanin Daurawa da Gwamnatin Kano

  • Rashin jituwar da ya shiga tsakanin hukumar Hisbah da gwamnatin jihar Kano na ci gaba da haifar da martani daga 'yan Najeriya musamman ma 'yan siyasa
  • Tsohon hadimin Buhari kuma jigon jam'iyyar APC, Ismaeel Buba Ahmed, ya yi tsokaci bayan murabus da Sheikh Aminu Daurawa ya yi daga shugabancin Hisbah
  • Da yake yaba ayyukan 'yan Hisbah, matashin 'dan siyasar ya yi fatan ganin an warware matsalar cikin gaggawa da lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Kano - Wani tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ismaeel Buba Ahmed, ya yi martani akan sabanin da ya shiga tsakanin hukumar Hisbah ta Kano da gwamnatin jihar.

Alaka dai ta yi tsami tsakanin gwamnatin Abba Kabir Yusuf da hukumar Hisbah a jihar Kano, inda har gwamnan ya fito ya soki ayyukan hukumar a bainar jama'a.

Kara karanta wannan

Hisbah Kano: Tsohon hadimin Buhari ya magantu kan murabus ɗin Sheikh Daurawa

Jigon APC ya yi tsokaci kan rikicin Daurawa da Abba
“Allah Ya Sa Malam Ya haqura”: Jigon APC Ya Magantu Kan Sabanin Daurawa da Gwamnatin Kano Hoto: @daily_trust, @ibrahim_daurawa, @IsmaeelAhmedB
Asali: Twitter

Lamarin ya yi zafi ta yadda har sai da Shugaban Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi murabus daga kujerarsa, a ranar Juma'a, 1 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Allah ya sa mallam ya haqura - Buba Ahmed

Da yake martani kan haka a shafinsa na X, matashin ‘dan siyasar ya nuna muradinsa na son ganin an yi sulhu tsakanin gwamnatin Abba da kuma Shehin malamin.

Buba Ahmed ya kuma yaba da jajircewar hukumar Hisbah na tsayawa tsayin daka kan wasu muhimman batutuwa a jihar Kano.

Ya kuma roki Allah ya sa Sheikh Daurawa ya hakura domin a cewarsa, malamin na aikin alheri da kawo gyara ne.

Ya rubuta a shafinsa cewa:

"Ina fatan za a warware rashin fahimtar da ke tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Malam Daurawa cikin gaggawa da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya karya gwiwar Sheikh Daurawa, ya yi murabus daga shugabancin Hisbah

"Na gamsu musamman da yadda Hisbah ta dage kan wasu muhimman batutuwa a Kano. Allah ya sa Malam ya haqura saboda suna yin aiki mai kyau."

Bashir Ahmed ya magantu kan murabus din Daurawa

A gefe guda, mun ji a baya cewa tsohon hadimin Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, ya yi tsokaci kan murabus din Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa daga shugaban hukumar Hisbah Kano.

Bashir Ahmad ya ce "Abba ya kwancewa Hisbah zani a kasuwa" shi ya sa Sheikh Daurawa ya hakura ya ajiye aikin na sa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel