Za mu yi amfani da lambar BVN don binciko talakawa masu bukatar tallafi - Minista

Za mu yi amfani da lambar BVN don binciko talakawa masu bukatar tallafi - Minista

Gwamnatin tarayya ta ce za ta yi amfani da lambar tantance asusun banki (BVN), wajen gano talakawa da gajiyayyun 'yan Najeriya, domin basu tallafin rage radadi.

Ministar Jin dadi da Walwalar jama'a, Sadiya Farouq, ta bayyana hakan a jiya Talata, 21 ga watan Afrilu, a Abuja, a lokacin taron kwamitin fadar Shugaban kasa kan COVID-19.

Ta bayyana cewa ta wannan hanyar za a fi saurin yin rabon cikin sauki.

Ta ce, “Za mu yi amfani da wasu hanyoyi ciki harda lambar tantance asusun banki wato BVN.“

“ Za kuma mu yi amfani da layukan sadarwa wajen gano talakawa da gajiyayyu a kasar. Wannan zai fi sauri, zai kasance a bayyane sannan kuma zai fi sauki wajen lissafi.”

Za mu yi amfani da lambar BVN don binciko talakawa masu bukatar tallafi - Minista

Za mu yi amfani da lambar BVN don binciko talakawa masu bukatar tallafi - Minista
Source: Facebook

Ministar ta kara da cewa tsarin rabon kudi na hannu da hannu zuwa ga talakawa wanda ke gudana a yanzu a wasu yankunan kasar, yana tafiya ne bisa tsari kuma a bayyane.

A nashi bangaren, ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya bayyana cewa gwamnati ta gabatar da sabbin hanyoyin wayar da kai domin hana yaduwar annobar COVID-19.

Ya bayyana cewa ma'aikatar ta fito da sabbin hanyoyin wayar da kai na gidajen talabijin da rediyo, domin isar da sakonni ga yan Najeriya kan yada za su kare kansu da kuma guje ma kamuwa da cutar.

Ya yi bayanin cewa an shirya wadannan kiraye-kirayen ne cikin harsunan Turanci, Hausa, Igbo da kuma Yarbanci, an kuma fara haskawa a tashar NTA da FRCN.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Magungunan gargajiya sun taimaka wajen warkar dani – Kakakin majalisar Edo Frank Okiye

Gabanin yanzu, Bola Tinubu, ya bukaci gwamnatin tarayya (FG) ta yi amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) wajen aika wa 'yan Najeriya kudin tallafin rage radadin matsin da annobar covid-19 ta haifar.

Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya bayar da wannan shawara ne a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Laraba a Legas.

Ya ce za a iya biyan kudi kai tsaye zuwa asusun wadanda za su ci moriyar tallafin ta hanyar amfani da BVN dinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel