Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 5 da Aka Dakatar da Su Saboda Sun Yi Amfani da Ƙwayar Ƙarin Kuzari

Yan Wasan Ƙwallon Ƙafa 5 da Aka Dakatar da Su Saboda Sun Yi Amfani da Ƙwayar Ƙarin Kuzari

  • An dakatar da Paul Pogba, tsohon dan wasan Manchester United daga buga kwallon kafa na tsawon shekaru hudu bayan da ya fadi gwajin kwayoyi
  • Dakatar da Pogba ya nuna karyewar kadarin dan wasan da ya taba zama dan wasan kwallon kafa mafi tsada a duniya
  • Wannan labarin na Legit Hausa ya kawo jerin sunayen wasu fitattun 'yan wasa biyar da suka fuskanci dakatarwa a lokacin da suke taka leda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, kotun hukunta manyan laifuka ta Italiya ta dakatar da tauraron dan kwallon Faransa Paul Pogba na tsawon shekaru hudu.

Wata kotun hukunta 'yan wasa ta Italiya (NADO Italia) ta dakatar da Pogba na dan lokaci a watan Satumba bayan gwajin 'testosterone', da aka haramta amfani da shi, in ji AlJazeera.

Kara karanta wannan

An dakatar da Paul Pogba daga buga wasa na shekaru hudu, an fadi dalili

'Yan Kwallon kafa 5 da aka dakatar da su saboda amfani da kwayoyi masu kara kuzari
Pogba ya shiga sahun su Maradona wadanda aka dakatar da su saboda amfani da kwayoyi masu kara kuzari. Hoto: David Cannon/Allsport, Gabriele Maltinti/Getty Images, belN SPORTS
Asali: Getty Images

Bayan nasarar da Juventus ta samu a gasar Seria A da ci 3-0 a Udinese ranar 20 ga watan Agusta, aka gano sinadarin testosterone, wanda ke kara karfin 'yan wasa a jikin Pogba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake mayar da martani kan hukuncin, dan wasan na Faransa ya jaddada cewa akwai kuskure a wannan hukunci da aka yanke masa, DailyMail ta ruwaito.

Da wannan dakatarwar, Pogba ba zai taka leda ba har sai kakar 2027-28, lokacin da zai cika shekaru 34.

Ga jerin wasu manyan taurarin ƙwallon ƙafa waɗanda aka dakatar da su saboda amfani da sinadaran ƙara kuzari:

Diego Maradona

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, kwamitin ladabtarwa na gasar Italiya ta dakatar da Diego Maradona daga buga kwallon kafa na tsawon watanni 15 a watan Maris 1991.

An dakatar da Maradona ne saboda amfani da hodar iblis kafin wasan gasar SC Napoli da Bari. FIFA ta tsawaita dakatarwar tasa a fadin duniya bayan sauraron karar.

Kara karanta wannan

Hukumar kwallon kafa ta Saudiyya ta dakatar da Ronaldo da cin tararsa kan dalili 1, an yaɗa bidiyon

Andre Onana

A shekarar 2021, hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA, ta dakatar da golan Manchester United Andre Onana na tsawon shekara daya saboda shan kwayoyi masu kara kuzari.

Onana ya yi ikirarin cewa "a bisa kuskure" ya sha maganin matarsa ​​bayan ya ji zazzabi a jikinsa, wanda ya sa aka samu sinadarin 'diuretic furosemide' a cikin fitsarinsa.

Andrian Mutu

A shekara ta 2004, bayan ya bar Barcelona zuwa Ingila, an dakatar da Mutu na tsawon watanni bakwai bayan samunsa da laifin shan wani haramtaccen abu.

Hakazalika, a cikin 2010, yayin da yake taka leda a Fiorentina, Kotun Koli ta Italiya (Coni) ta dakatar da dan Romanian na tsawon watanni tara saboda gaza tsallake gwajin kwayoyi sau biyu.

Samir Nasri

An dakatar da tsohon tauraron Faransa Samir Nasri na tsawon watanni 18 a cikin 2018 saboda 'ledar ruwan magani' da ya sha a asibitin Los Angeles a 2016.

Kara karanta wannan

Babban labari: Gwamnatin Najeriya ta cafke jami'an manhajar Binance, an samu ƙarin bayani

An rage wa'adin dakatarwar haramcin na watanni 18 zuwa Yuli 2017, wanda ya sa ya dawo taka leda a watan Janairun 2019.

Kolo Toure

A watan Mayun 2011 yayin da Kolo Toure yake taka leda a Manchester City, aka dakatar da shi na tsawon watanni shida saboda amfani da sinadarin karin kuzari.

Tsohon tauraron dan kasar Ivory Coast ya amince da shan kwayar abincin matarsa.

Sai dai hukumar kwallon kafa ta Ingila a Wembley ta yanke hukuncin cewa Toure bai yi niyyar kara kuzari a wasanni ba, don haka aka janye dakatarwarsa zuwa watan Maris.

Yan wasan ƙwallon ƙafa da suka taba zaman gidan yari

A hannu daya kuma, Legit Hausa ta yi bayani kan wasu ƴan wasan ƙwallon ƙafa na duniya da ka taba yanke wa hukuncin zaman gidan yari.

Akalla ƴan wasa 10 ne suka yi zaman gidan yarin, ciki har da Ronaldinho wanda aka kama da laifin amfani da fasfo na bogi tare da dan uwansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.